Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya ta kaddamar da sabon tsarin jin dadin ma’aikata

WhatsApp Image 2026 08 05 at 8.23.47 AM 1785917483 1 750x430

Babban Kwantirolan Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, Olumode Adeyemi, ya sanar da kaddamar da Tsarin Tallafin Lafiya da sauran tsare-tsaren jin dadin ma’aikata, ciki har da kara kudin bashin da ba ruwa daga Naira 300,000 zuwa Naira 500,000.

Adeyemi ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin kaddamar da sabon Quarter Guard a Hedikwatar Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya dake Wuse a Abuja.

Ya ce ya gabatar da wadannan matakai ne jim kadan bayan ya karbi mukami domin inganta walwalar jami’ai.

A cewarsa, jin dadin ma’aikata ya kasance fifiko na farko tun bayan da ya karbi jagorancin hukumar.

“Daya daga cikin alkawarin da na yi wa jami’ai na shi ne ba da fifiko ga jin dadin ma’aikatan mu,” in ji shi.

Babban Kwantirolan ya bayyana cewa ya ki amincewa da wani babban taro na maraba da shi da abokansa a Najeriya da kasashen waje suka shirya masa, sannan ya juya kudin domin inganta jin daɗin ma’aikatan kashe gobara.

“Na ki wani taro mai kyau da abokaina suka shirya a gida da waje. Daga nan sai aka juya kudin aka sayi matoci da sauran kayayyaki domin tallafa wa ma’aikatan kashe gobara a fadin Najeriya,” in ji shi.

Kan Tsarin Tallafin Lafiya, Adeyemi ya bayyana cewa an tsara shi ne domin rage nauyin kudin magani ga jami’ai.

“Na kuma kaddamar da Tsarin Tallafin Lafiya inda jami’ai karkashin umurnina suka samu tallafin da ya rage musu kudin magani,” in ji shi.

Ya kara da cewa hukumar ta kuma fadada tsarin bashin da babu ruwa a ciki.

“Bashin da babu ruwa ya karu daga Naira Dubu Dari Uku zuwa Naira Dari Biyar, da sauransu,” in ji shi.

Adeyemi ya ce sauye-sauyen jin dadin ma’aikata sun inganta kwarin gwiwa sosai, inda ya bayyana cewa jami’ai da kansu ne suka tara kudi suka gina Quarter Guard da aka kaddamar a ranar Talata ba tare da wani umarni daga shugabanni ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here