Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara a ranar Asabar, ta bayyana cewa ta dawo da dukkanin motocin da ta ƙwace daga wajen tsohon gwamnan jihar Bello Matawalle.
kakakin rundunar, ASP Yazid Abubakar, shine ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) hakan a wayar tarho ranar Asabar.
Kotun wacce mai shari’a Aminu Bappah-Aliyu, ke jagoranta a ranar 15 ga watan Yuni, ta bayar da umarni ga dukkanin hukumomin tsaron da suka ɗauko motoci a gidajen Matawalle na Gudau da Maradun da su mayar da su cikin sa’o’i 48.
Jami’an tsaron dai sun ɗauko motocin ne daga gidajen guda biyu bisa umarnin gwamnatin jihar.
Abubakar ya tabbatar da cewa babu sauran mota ko guda ɗaya ta tsohon gwamnann a hannunsu domin duk sun mayar da su.
“Eh tabbas, rundunar ƴan sanda ta bi umarnin kotu dangane da mayar da dukkanin motocin tsohon gwamna Bello Matawalle.”
“Mun mayar da dukkanon motocin zuwa harabar babbar kotun tarayya a Gusau. A yanzu da na ke maganar nan, babu mota ko guda ɗaya a hannun ƴan sanda.”












































