Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta kama wani matashi bisa zargin kashe kishiyar babarsa da ‘yarta mai shekara takwas.
A wata sanarwa da kakakin ‘yan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce lamarin ya faru ne a jiya Asabar a Fadama Rijiyar Zaki da ke Karamar Hukumar Ungogo bayan da mahaifin matashin ya dawo ya sami matarsa da ‘yarsa cikin jina-jina.
Sanarwar ta ƙara da cewa bayan da rundunar ‘yan sandan jihar ta samu labarin abin da ya faru, nan take ta aika jami’anta zuwa wajen inda bayan an kai matar da kuma ‘yarta Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad ne likita ya tabbatar da rasuwarsu.
An dai kama wanda ake zargin ne mai suna Gaddafi a wani gida da ba a kammala ba a kokari da yake na tserewa ya bar jihar.
A binciken farko da aka gudanar, wanda ake zargin ya amsa laifinsa na yin kisan inda ya ce ya yi amfani da sukun-direba wajen daɓawa kishiyar babarsa a wuya da kuma kai sannan ta shake ‘yarta da ɗankwali har sai da ta daina numfashi.













































