Rashin Tsaro: Majalisar Wakilai ta nemi hadin kan hukumomi don yaki da biyan kudin fansa

Reps new 750x430

Majalisar Wakilai ta umarci Shugaba Bola Tinubu da ya samar da tsarin hadin gwiwa tsakanin hukumomi domin yaki da biyan kudin fansa a kasar.

Wannan ya biyo bayan amincewa da wani kuduri da Dan majalisa Ademorin Kuye na APC daga jihar Legas ya gabatar a zaman majalisar na ranar Laraba a Abuja.

Majalisar ta jaddada bukatar karfafa bayanan hada-hadar kudi da hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, masu kula da tsari da cibiyoyin kudi domin katse hanyoyin da ake bi wajen biyan kudin fansa. Rahotanni sun nuna cewa an biya kusan Naira tiriliyan 2.23 matsayin kudin fansa tsakanin Janairu 2021 zuwa Yuni 2025.

Yayin da yake gabatar da kudurin, Kuye ya bayyana cewa Sassa na 14(2)(b) da na 33(1) na Kundin Tsarin Mulki sun bai wa Gwamnatin Tarayya babban alhakin kare rayuka, kiyaye doka da oda da kuma kare ikon tattalin arzikin Najeriya.

Ya kuma ce Dokar Babban Bankin Najeriya ta 2007 da Dokar Bankuna da Sauran Cibiyoyin Kudi BOFIA, sun ba CBN iko da kulawa kan manufofin kudi, sarrafa kudi da kuma tsarkake tsarin kudin kasar.

Dan majalisar ya ce Dokar Hana Halatta Kudaden Haramun ta 2022 da Dokar Hana Ta’addanci ta 2022 sun sanya wajibai a kan cibiyoyin kudi, kasuwancin da ba na kudi ba, da hukumomin gwamnatin da suka dace.
A cewarsa, dole ne su gano, bayar da rahoto da dakile hada-hadar kudi ba bisa ka’ida ba, ciki har da biyan kudin fansa.

“Rahotanni daga hukumar leken asirin harkokin kudi ta Najeriya (NFIU) da binciken kwarewar laifuka da fahimtar tsaro na ofishin kididdiga na kasa (CESPS) na 2024 da kuma kungiyoyin bincike masu zaman kansu kan tsaro sun nuna cewa ‘yan Najeriya sun biya kusan Naira tiriliyan 2.23 a matsayin kudin fansa tsakanin Janairu 2021 zuwa Yuni 2025,” in ji shi.

Kuye ya ce wannan ya taimaka wajen ci gaba da garkuwa da mutane da sauran ayyukan manyan masu laifi.

“Binciken da Cibiyar Yaki da Ta’addanci ta Kasa (NCTC), karkashin Ofishin Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro (ONSA) ta yi, ya nuna cewa masu sana’ar POS da sauran hanyoyin kudi ana amfani da su wajen biyan kudin fansa da kuma boye hanyoyin kudi, wanda hakan na kawo cikas ga kokarin dawo da kudi da binciken jami’an tsaro.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here