Gwamnatin Katsina ta kafa kwamitin bincike akan Kisan Mai gari

dikko
dikko

Gwamnatin Jihar Katsina ta kafa kwamitin bincike akan kisan gillar da akayi wa mai garin dabaibayawa da kae karamar hukumar batagarawa da ke jihar.

Ishaq Miqdad hadimin gwamna Dikko Radda, ya bayyana wannan jawabin a wata sanarwa daya fitar ranar Alhamis, ya kara da cewa kisan ya faru ne sati biyu da suka wuce.

Biyo bayan tashin hankula da mutanen garin suka shiga wanda yake da alaka da kisan gilla da kuma garkuwa da mutane, gwamnatin ta dauki matakin kafa kwamitin bincike, domin gano masu hannu a wannan ta’asa.

Miqdad ya kara da cewa “Kwamitin yana karkashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Malam Faruk Lawal-Jobe”

Bayan kaddamar da kwamitin ranar Alhamis, mataimakin gwamnan na jihar Katsina, ya bada umarnin a fara binciken gaggawa akan wannan al’amari, a kuma tabbatar an kamo masu laifin.

Malam Faruk ya kara da cewa kwamitin ya kunshi mutane daga hukumomi daban daban, kama daga kan ‘yan sandan sa kai, da na farin kaya, da wakilai daga hukumar ‘yan sanda ta jihar. Sauran sun hada da ma’aikatar shari’a, shugabancin kananan hukumomi, da masarautar jihar ta Katsina.

Ya kara da tabbacin cewar a sati biyu wannan kwamitin zai kawo rahoton binciken da suka hada domin gwamnati ta aiwatar da abinda day a kamata.
Daga karshe, masarautar Katsina ta mika godiya ga gwamnatin Jihar bisa jajircewa da nuna amanna ga wannan kwamitin.

(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here