Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa, NAFDAC, ta kama magunguna da kudinsu ya kai Naira miliyan 110 tare da cafke wasu mutane da ta ke zargi da safarar magungunan.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ruwaito cewa, ta samu nasarar ne a samamen da jam’ianta suka gudanar a wasu biranen kasar da suka hadar da Lagos da Kaduna da Abuja da kuma Asaba.
Haka kuma hukumar ta NAFDAC ta kara da cewa tana ci gaban da gudanar da bincike kan mutanen 15 da ta kama a kokarinta na dakile yaduwar magunguna marasa inganci da ba a yi wa rijista ba.
Sanarwar hukumar ta kuma ce, a yayin samamen hukumar ta kama magungunan da suka hada da oxytocin da tramadol da morphine da sauransu.
Haka kuma ta cikin sanarwar, shugabar hukumar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta gargadi ‘yan kasuwa da masu talla akan titi kan sayar da magungunan bogi, tana mai cewa za su fuskanci hukunci mai tsanani.
Haka kuma ta shawarci al’ummar kasar nan da su guji sayen magunguna daga hannun masu talla, tare da jaddada kudirin hukumar na tabbatar da samun inganci a fannin abinci da magunguna a fadin Najeriya.













































