Harin Masallatai: An kashe mutane 30, an sace fiye da 60 a Jihar Neja

Bandits. Photo Credit ZAgazola 750x430 (2)

A kalla mutane 30 aka tabbatar da mutuwarsu biyo bayan hare-haren da aka kai a masallatai hudu a Karamar Hukumar Borgu da ke Jihar Neja a ranar Juma’ar da ta gabata.

‘Yan ta’adda sun kai harin ne a lokaci guda a masallatan lokacin da ake gudanar da sallar Juma’a a garuruwan Dekara, Kpenya, Sabon Gida da Gidan Zana, inda suka yi awon gaba da dumbin masallata.

An bayyana cewa maharan sun tattara masallatan ne guri gaya sannan suka kora su zuwa cikin daji.

Da yake magana da jaridar Daily Trust a ranar Litinin, Shugaban Karamar Hukumar Borgu, Mohammed Nasir Abdullahi, ya tabbatar da cewa kimanin mutane 30 da aka sace an kashe su ne ta hannun wadanda suka yi garkuwa da su.

Ya bayyana cewa garuruwan a yankin sun gano gawarwakin wadanda abin ya shafa kuma an riga an binne su.

“Sojoji sun shiga yankin a yanzu. Ko’ina ya lafa. Mun rasa wasu mutane, kuma an yi jana’izarsu. Wasu mutanen kuma sun gudu zuwa wurare masu tsaro.”

“Bisa ga bayanan da nake da su, mutanen da aka sace sun kai sama da 60. Wadanda aka kashe kuma sun kusa 30,” in ji shugaban karamar hukumar.

Ya kara da cewa an kona wasu gidaje, ciki har da gidan Hakimin Dekara, Abubakar Umar, yayin hare-haren.

Shugaban ya ce an sace mutanen ne daga garuruwa hudu da aka ambata yayin da suke tsaka da gudanar da sallar Juma’a.

Biyo bayan hare-haren na ranar Juma’a, daruruwan mazauna yankunan sun tsere zuwa garin New Bussa da kuma Jamhuriyar Benin bayan da ‘yan ta’addan suka yi barazanar kashe duk wanda ya rage a wadannan al’ummomi.

“Mutane kadan ne kawai suka rage a Dekara yanzu. Yawancin mutane sun gudu,” in ji wani mazaunin yankin.

Rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa an kaddamar da aikin jami’an tsaro na hadin gwiwa domin gano maharan da kuma ceto masallatan da aka sace.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here