Mutane bakwai ne suka mutu a wani mummunan hadarin mota da ya auku a kan hanyar Bida zuwa Kutigi a Jihar Neja, in ji Hukumar Kula da Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC).
Kwamandan hukuar FRSC ta Jihar Neja, Aishatu Sa’adu, ce ta tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ranar Lahadi.
Sa’adu ta ce hadarin ya faru ne ranar Lahadi da yamma a kauyen Shebe, kilomita kadan daga garin Kutigi.
Ta ce hadarin ya rutsa da motar Mazda da kuma motar bas din Siena da ke tafiya a kan hanyar Bida zuwa Kutigi.
“Mutane bakwai sun rasa rayukansu, bakwai kuma sun jikkata yayin da aka ceto wasu hudu ba tare da rauni ba. Jimilla mutane 18 da abin ya rutsa da su,” in ji ta.
Kwamandan ta ce mutane bakwai ne suka mutu a wurin da hadarin ya faru, yayin da wasu bakwai suka samu raunuka daban-daban.
Ta ce an kai wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Gwamnati na Kutigi domin samun kulawar likitoci.
A cewar Sa’adu, an kuma ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiye gawa na Asibitin Kutigi.
FRSC bata bayyana sunayen wadanda abin ya rutsa da su ba kawo yanzu, kuma bata ba da karin bayani kan yadda hadarin ya faru ba.
Wannan lamarin ya sake nuna hatsarin da direbobi da fasinjoji ke fuskanta wajen amfani da hanyar Bida zuwa Kutigi, musamman wajen tafiya tsakanin manyan garuruwa.
Ana sa ran hukumomi za su binciki abin da ya haddasa hadarin tare da gano abubuwan da suka kai ga wannan mummunan hadari. (NAN)













































