Hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC), reshen Jihar Kano, ta ceto mutane 15 bayan wani hadarin mota da ya rutsa da wata motar DAF da ba a san lambar rijistarta ba a kan hanyar Kano zuwa Zaria.
Hukumar ta ce hadarin ya faru ne da misalin karfe 5:00 na asubayin ranar Lahadi da Gadan Yankifi.
Kwamandan FRSC na Jihar Kano, Idris Lawal ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Abdullahi Labaran ya raba wa manema labarai a ranar Lahadi a Kano.
Lawal ya ce “Mun samu kiran gaggawa da misalin karfe 5:00 na asuba a ranar Lahadi daga wani mai kishin kasa.
“Da muka samu rahoton, nan da nan muka tura tawagar cetonmu zuwa inda hadarin ya faru cikin mintuna biyar.
“Hadarin ya hada motar DAF da ke dauke da fasinjoji da kayayyaki.
“An dauke wadanda hadarin ya rutsa da su mutum 15 zuwa Asibitin Kura na Gwamnati domin samun kulawar likitoci. Babu wanda ya mutu a cikin hadarin.”
Ya shawarci masu amfani da hanyar Kano zuwa Zaria da su yi hakuri, su rage gudu yayin da suka zo kusa da wurin, kuma su bi dokoki da ka’idojin hanya.
Kwamandan ya kuma bukaci direbobi da su ba jami’an FRSC da sauran masu ba da agajin gaggawa hadin kai a wurin da hadarin ya faru.
Lawal ya tabbatar wa al’umma baki daya cewa ana ci gaba da kokarin tsaftace hanyar domin a dawo da zirga-zirga kamar yadda aka saba. (NAN)













































