Kano ta samu yara 875,593 da ba sa zuwa makaranta a shekarar 2026 – Hukuma

Out of School children sabo 671x430

Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta ce jihar ta samu yara 875,593 da ba sa zuwa makaranta (OOSC) a cikin rahoton binciken da aka yi a shekarar 2026.

Wannan na kunshe ne cikin sanarwar da Darakta mai kula da yada labarai na ma’aikatar, Musbahu Aminu Yakasai, ya fitar a ranar Juma’a a Kano.

Aminu Yakasai ya ce Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dr. Ali Haruna Makoda, ne ya bayyana haka yayin gabatar da rahoton binciken yaran da ba sa zuwa makaranta na Jihar Kano na 2026.

Haruna Makoda ya ce sabon adadin ya nuna raguwar mutane 113,641 wato kashi 11.5, idan aka kwatanta da yara 989,234 da UNICEF ta bayyana a shekarar 2023.

Ya ce wannan raguwa shaida ce ta gudummawa da aka dade ana yi da kuma saka jari a fannin ilimi na haifar da sakamako mai kyau.

Sai dai Kwamishinan ya ce adadin yaran da har yanzu ba sa zuwa makaranta yana nuna cewa ana bukatar kara kokari da hafin kai.

Ya ce “Adadin da aka gabatar a baya galibi kiyasin da aka yi ne daga samfurin kasa da sauran majiyoyi. Amma adadin na 2026 an samo shi ne daga cikakken bincike da aka yi a fadin jihar.
Binciken ya ba da cikakkun bayanai da aka raba su ta Kananan Hukumomi, shekaru da jinsi.”

Ya ce sabon bayanan zai zama ginshiki mai inganci don tsara ilimi bisa hujja, tsara manufofi, raba kayayyaki da kuma kirkirar hanyoyin da za a bi na shigar da yaran da ba su cikin tsarin karatun gwamnati makaranta da kuma rike su.

Kwamishinan ya danganta wannan ci gaba ga kudurin gwamnatin jihar karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, musamman kara saka jari a fannin ilimi.

Ya ce habaka shigar yara makaranta, karfafa tsarin tattara bayanan ilimi da hadin kai da UNICEF da sauran abokan hulda sune manyan abubuwan da suka taimaka wajen magance matsalar.

Haruna-Makoda ya roki masu ruwa da tsaki da su yi amfani da sakamakon binciken wajen tsara mafita da ta dace da bukatun al’ummomi da Kananan Hukumomi.

Ya kara da cewa duk da raguwar adadin yana da dadi, amma har yanzu adadin yaran da ba sa zuwa makaranta yana nuna cewa ana bukatar karin aiki.

“Tare da ingantattun bayanai, ci gaba da saka jari, hadin gwiwa mai karfi da niyyar siyasa, za mu iya rage wannan matsala sosai,” in ji Haruna-Makoda.

Ya sake jaddada aniyar ma’aikatar wajen karfafa amfani da ingantattun bayanai wajen tsarawa, sanya ido da rabon albarkatu a fannin ilimi a fadin jihar.

Ya ce yada wannan rahoto muhimmin mataki ne na karfafa hadin kai da masu ruwa da tsaki da kuma habaka kokarin tabbatar da cewa kowane yaro a Kano ya sami damar zuwa makaranta.

Kwamishinan ya yi kira ga iyaye, sarakuna, malaman addini, al’ummomi, abokan ci gaba da kungiyoyin al’umma da su kara goyon bayan gwamnati ta hanyar karfafa iyalai su shigar da ‘ya’yansu makaranta su kuma ci gaba da kasancewa. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here