Majalisar wakilan Najeriya za ta gana da kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU da sauran masu ruwa da tsaki domin kawo karshen yajin aikin da kungiyar ke yi.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da magatakardan majalisar, Yahaya Danzaria ya fitar yau a Abuja, ya ce taron zai gudana ne a gobe Talata a majalisar wakilai ta kasa.
Majalisar ta dauki matakin ganawa da ƙungiyar malaman jami’a da ministan ilimi sakamakon yajin aikin da aka shafe watanni bakwai ana yi.
Takardar gayyatar da aka aikewa kungiyar an bukaci shugabanci da sauran masu ruwa da tsaki su hallara a zauren majalisar gobe domin kawo karshen yajin aikin.
Majalisar ta roƙi shugabancin malaman jami’a ASUU da sauran masu ruwa da tsaki su bayyana a gabanta domin kawo karshen matsalar baki daya.













































