Gwamnatin Tarayya ta gano Jami’o’in bogi kusan 70-Adamu Adamu

Adamu Adamu
Adamu Adamu

Gwamnatin tarayya ta ce hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) ta gano jami’o’i kusan 70 da suka sabawa doka da kuma kwalejojin ilimi kusan 125 da ke aiki a kasar nan.

Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin taron karawa juna sani na majalisar Zartarwar Kasar nan karo na 47 a Abuja.

Adamu ya ce haramtattun jami’o’in da ya bayyana a matsayin “Degree Mills” na kawo babban kalubale ga kokarin da ma’aikatar ke yi na ganin an samu damar samun ilimin jami’a ba tare da wata matsala ba.

A bayanan karshe da hukumar ta NUC ta wallafa dangane da makarantun boko da cibiyoyin karatun da aka yi su ba bisa ka’ida ba, a shekarar 2021, hukumar ta bayyana sunayen jami’o’i 58 da ta rufesu da kuma jerin sunayen wasu cibiyoyi 8 da har yanzu ake ci gaba da bincike kan zargin kasancewarsu na bogi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here