Sojoji sun kama wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a Kaduna

IMG 20220817 WA0147 750x430 1
IMG 20220817 WA0147 750x430 1

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kama wasu mutane bakwai da ake zargin ‘yan bindiga ne a kauyen Mariri da ke karamar hukumar Lere a jihar.

A wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar a ranar Larabar ta ce kama daya daga cikin wadanda ake zargin tare da kashe shi yana kunshe ne a cikin wani rahoto da hukumomin tsaro suka gabatar.


A cewar rahoton, an kama mutanen ne bayan tattara bayanan sirri.

Rundunar ta ce dakarun Operation Safe Haven sun yi aiki da sahihan bayanan sirri, inda suka kama wasu ‘yan kungiyar masu garkuwa da mutane, masu suna Musa Adamu da Abdullahi Usman da Suleiman Hasidu sai Usman Jibril da Saidu Isah da Hassan Abdulhamid da kuma Idris Sani.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here