Gwamnatin tarayya, a ranar Laraba, ta shaidawa wata babbar kotun tarayya dake Abuja cewa shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya zabi ya ci gaba da gurfana gaban kotun ne cikin irin kayan da ya saba sanyawa.
Lauyan gwamnatin tarayya. Shuaibu Labaran, ya shaida wa mai shari’a Binta Nyako hakan jim kadan bayan fara zaman.
“An dage shari’ar zuwa yau Laraba domin gurfanar da shi a gaban kuliya.
“Amma kafin lokacin, ina son yardar ku da saboda kun ba da umarnin kada wanda ake tuhuma ya sake bayyana a cikin wannan tufafin.
“Amma wanda ake kara (Kanu) ya zabi sanya tufafi iri daya,” in ji shi.
Labaran ya kuma shaida wa kotun cewa hukumar ta DSS ta bi umarnin kotu ta hanyar sayo wa shugaban kungiyar IPOB katifa da matashin kai don jin dadin tsare shi.
Sai dai Lauyan Kanu, Cif Mike Ozekhome, SAN, ya ki yarda cewa wanda yake karewa bai ki saka wani kaya ba.
Ya ce sun samo masa wasu tufafin a jiyan kafin, amma kafin su kawo masa lokaci ya kure.
Ya kuma tabbatar da cewa a ranar da kotun zata sake zama, Kanu zai bayyana a cikin wata tufafi.
Don haka Ozekhome ya yabawa hukumar DSS bisa bin umarnin kotu ta hanyar siyo wa wanda yake karewa katifa da matashin kai da nufin samun sauki.
Mai shari’a Nyako ta ce za a iya mika kayan ga jami’in shari’a da suka zo cikin kayan jami’an tsaro.
Muna tafe da cikakken bayani nan gaba.












































