‘Yan kasuwar dabbobi a Jihar Kano na kuka kan rashin kasuwa a manyan kasuwanni gabanin bikin Idin Babbar Sallah, duk da tsammanin samun karuwa a harkokin kasuwanci a duk lokacin bukukuwan Sallar.
A ziyarar da muka kai kasuwar dabbobi ta Kofar Mazugal ta nuna karancin masu saya da harkokin kasuwanci, lamarin da ‘yan kasuwa suka bayyana a matsayin wanda ba a saba gani ba idan aka kwatanta da shekarun baya.
Shugaban kasuwar, Mallam Muhammad Chika, ya ce ‘yan kasuwa na cikin damuwa saboda karancin masu zuwa saye, inda ya bayyana cewa da yawa daga cikin masu sayarwa sun yi kwanaki a kasuwa ba tare da samun kasuwa ba.

A cewarsa, matsin tattalin arziki da raguwar karfin saye na iya zama abin da ke hana mutane da yawa siyan dabbobi domin bikin Sallah.
“Babu ciniki mai yawa a wannan shekara, duk da an saukaka farashi, mutane ba sa zuwa siye kamar yadda ake tsammani,” in ji shi.
Chika ya yi fatan cewa kasuwa na iya karuwa yayin da bikin Sallar ya gabatowa sosai, amma ya yarda cewa yanayin da ake ciki yanzu ya haifar da rashin tabbas a tsakanin ‘yan kasuwar dabbobi.
Wasu ‘yan kasuwa da suka yi zanta da SolaceBase sun ce lamarin na nuni da yadda matsin tattalin arzikin da ke fuskantar ‘yan Najeriya da yawa.
Guda daga cikin masu sayar da dabbobin, Habibu Aliko Koki, ya ce karancin masu saya na shafar kasuwanci a duk harkokin kasuwar, inda ya kara da cewa da yawa daga cikin ‘yan kasuwa suna fama wajen mayar da kudin da suka saka don siye da ciyar da dabbobin.
“Ba harkar dabbobi kadai yanayin nan ya shafa ba, za ka iya ganin bambanci tsakanin wannan shekara da shekarar da ta gabata,” in ji shi.
Koki ya bayyana cewa tashin farashin abincin dabbobi ma ya kara tsananta lamarin ga masu sayarwa, domin kiwon da dabbobi ya yi tsada.
Wani dan kasuwa, Auwalu Sani Salisu, ya danganta rashin ciniki da tunanin jama’a cewa farashin dabbobi ya wuce karfin masu matsakaicin hali.
Ya bayyana cewa duk da koke-koken da ake yi kan tsadar farashi, ‘yan kasuwa na fuskantar karuwa tsadar kaya, musamman na ciyarwa da sufuri.
Masu saya a kasuwar ma sun yarda da karancin masu zuwa, inda wasu suka ce iyalai da yawa na iya zama ba su shirya ta fuskar kudi ba don yin layya a wannan shekara.

SolaceBase ta lura cewa sassa da dama na kasuwar sun kasance babu cunkoso a lokacin ziyar, inda da yawa daga cikin ‘an kasuwa ke jiran abokan ciniki yayin da bikin Idin Babbar Sallah ke gabatowa.












































