Tinubu ya nada sabon Shugaba a hukumar JAMB

Bola Tinubu signs 750x430

Shugaba Bola Tinubu ya nada Prof. Segun Aina a matsayin sabon Rijista na Hukumar Shirya Jattabawar Shiga Jami’a da Manyan Makarantun gaba da Sakendire (JAMB), inda zai gaji Prof. Is-haq Oloyede.

Wa’adinsa na Oloyede zai kare 31 ga Yuli.

Aina, wanda zai cika shekara 40 a watan Yuli, masanin kuma kwararren malami wanda kwararre ne a fannin tsarin kwamfuta, ya kuma gogewa mai yawa a fannin tsarin jarrabawa, ababen more rayuwa na dijital, gyara cibiyoyi, da sauyi na aiki wanda ya dogaro da fasaha a bangaren gwamnati a fadin Najeriya.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai Magana da yawun Shugaban Kasa, Mista Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis a Abuja.

Aina yana da digirin farko na Injiniyanci a fannin Kwamfuta daga Jami’ar Kent, kuma ya samu duka digiri na biyu da na uku daga Jami’ar Loughborough da ke Burtaniya.

Ya samu MSc a fannin Internet Computing da Network Security da PhD a fannin Digital Signal Processing, kafin ya kammala shirin Senior Management Programme a Lagos Business School.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here