Rundunar sojin Najeriya Sashe na II na Operation FANSAN YAMMA sun kama wanda ake zargi da samar da kayan tallafi ga kungiyoyin ’yan ta’adda, sun kuma kwato takalman yaki 150 da sauran kayan aikin soja a Jihar Zamfara.
Hakan na cikin rahoton da rundunar da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya samu a ranar Alhamis.
A cewar rahoton, an kama wanda ake zargin ne a kan babbar hanyar Sokoto zuwa Gusau yayin duba motoci da sojoji suke gudanarwa a ranar Laraba.
Sojojin sun ce wanda ake zargin yana tafiya ne da motar Honda Civic lokacin da suka gano tarin kayan aikin soja da a boye a cikin motar.
“Kayan da aka kwato daga wurin wanda ake zargin sun hada da takalman yaki 150, wukaken da ake nadewa 3, na’urar girgizar jiki 3, kwanson hayaki ma isa hawaye 1, hula ta soja 1 da bel 1.
“Sojoji sun kuma kwato wayoyin Android guda 2, iPad 1 da agogon hannu na dijital da ake ganin suna da mahimmanci ga bincike,” in ji rahoton.
Rahoton ya bayyana kama mutumin a matsayin wata babbar nasara a kokarin da ake na rushe hanyoyin samar da kayan tallafi ga ’yan ta’adda da ’yan bindiga a fadin Arewa maso Yamma.
Ta bayyana cewa dakatar da jigilar kayan aiki da tallafi ga masu laifi yana da matukar muhimmanci wajen raunana karfin aikinsu da kuma hana su kaddamar da hare-hare.
A cewar rahoton, wanda ake zargin yana hannun sojoji ana ci gaba da bincike, yayin da kayan da aka kwato aka ajiye su a matsayin shaida.
Sojojin sun kara da cewa wannan aiki ya nuna tasirin duba motoci da ake kara yi a karkashin Operation FANSAN YAMMA domin hana ‘yan ta’adda samun ‘yancin motsi da samun kayan aiki na yaki.
Ta sake jaddada aniyar Sojojin Najeriya na ci gaba da matsa lamba ga kungiyoyin ‘yan ta’adda da masu goyon bayansu domin dawo da zaman lafiya da tsaro a Jihar Zamfara da Arewa maso Yamma baki daya. NAN













































