Shugaba Bola Tinubu ya taya Murtala Sule Garo murna kan rantsar da shi a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano da aka yi.
SolaceBase ta ruwaito cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya rantsar da Garo a ranar Talata bayan nadinsa don cike gurbin da murabusin Aminu Abdussalam Gwarzo ya bari.
A cikin wata sanarwa da Mai Ba shi Shawara na Musamman kan Harkokin Yada Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaban ya yaba wa Yusuf kan nadin Garon, inda ya bayyana shi a matsayin mataki da ke karfafa hadin kai a cikin Jam’iyyar APC a Jihar Kano.
Tinubu ya yi wa Garo fatan nasara a sabon mukaminsa kuma ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a jihar da su mara wa gwamna da mataimakinsa baya domin tabbatar da gudanar da mulki mai inganci.
Ya kuma shawarci sabon mataimakin gwamnan da ya yi aiki tare da gwamna domin samar da mulki mai kyau da kuma hanzarta ci gaban jihar.
Garo ya rike mukamai da dama na gwamnati a baya, ciki har da Shugaban Karamar Hukumar Kabo da Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu a zamanin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje.
Dan shekara 48 din ya kuma kasance mataimakin dan takar gwamna na APC a babban zaben shekarar 2023.










































