Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da kiyaye sauye-sauyen ilimi da aka fara a karkashin shirin hadin gwiwar koyo ga kowa a Najeriya (PLANE) da Gwamnatin Burtaniya ke tallafawa, yana mai cewa ilimi shine ginshikin cigaban jihar domin gobe.
Wannan na cikin wata sanarwa da Daraktan yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Asabar.
Gwamna Yusuf ya bayyana matsayar tasa ne ta bakin Kwamishinan Ilimi, Dr. Ali Abubakar Haruna Makoda, wanda ya wakilce shi a taron sauya salon shirin PLANE da aka gudanar a Kano a ranar Alhamis.
Gwamna Yusuf ya ce gwamnatinsa za ta kara karfafa nasarorin da aka samu a cikin shirin na shekaru biyar ta hanyar inganta tsare-tsaren ilimi, habaka horar da malamai, kara samun kayan koyo masu inganci da tabbatar da cewa kowane yaro ya samu ilimi mai inganci.
Ya yaba wa Ma’aikatar Harkokin Waje, Kungiyar Kasashe Renon Burtaniya (Commonwealth) da ta Ci Gaban Burtaniya (FCDO), shirin PLANE, ta Tseratar da Yara ta Duniya da sauran abokan aiki kan gudummawarsu mai matuƙar muhimmanci wajen sauya fannin ilimi a Kano.
Gwamnan ya ce shirin ya taimaka wa jihar wajen samun sahihin bayanai kan yaran da ba sa zuwa makaranta ta hanyar cikakken bincike, lamarin da ya bai wa gwamnati damar yin tsare-tsare na musamman domin rage adadin yaran.
Ya kuma yaba da gudummawar PLANE wajen inganta karatu da rubutu da kuma lissafi na asali ta hanyar horar da malamai da samar da kayan koyarwa a makarantun jihar.
Gwamna Yusuf ya tabbatar wa abokan ci gaba da cewa Jihar Kano za ta mayar da sauye-sauyen da aka fara a ƙarƙashin shirin na dindin, tare da ci gaba da saka jari a manufofi da tsare-tsaren da za su inganta sakamakon koyo na yara











































