Kaddamar da Hukumar Hadin Gwiwa don Yaki da Shaye-shaye da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Jihar Kano na iya zama daya daga cikin muhimman matakan tsaro na gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar.
Ya zama tamkar daukar mataki ne kan wani lamari da ya addabi mazauna jihar, wanda suke ganin kamar lamarin na shaye-shaye ya zama wani batu da ake yi wa kallon bana lafiya ba.
Ya zama babbar matsala a tsarin zamantakewa, tattalin arziki da tsaro wanda ke barazana ga zaman lafiya, ayyuka da makomar Jihar Kano.
Tsawon shekaru, al’ummomi a Kano na fama da matsaloli sakamakon shaye-shaye a tsakanin wasu matasa.
Illolinsa na bayyana ne ta hanyar karuwar fashi da makami, kwacen waya, fashi a titi, haura gidaje da sauran ayyukan ta’addanci da suke tada hankali a unguwanni.
Duk da cewa zai iya zama abu mai sauki kuma wanda yake ba daidai ba a danganta dukkan wani sakamakon laifi da shaye-shaye, haka kuma rashin adalci ne mu yi watsi da rawar da miyagun kwayoyi ke takawa wajen tayar da tarzoma, lalata tunani, karfafa dabi’a mara kyau da kuma ingiza masu ta’ammali da shi aikata laifuka.
Kididdiga ta nuna cewa, shekarar 2021, Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), Birgediya-Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya bayyana cewa Kano na da kashi 16 cikin 100 na masu shaye-shaye a tsakanin mutane daga shekaru 15 zuwa 64.
A cewarsa, kusan mutum miliyan 2 a jihar suna shan kwayoyi, musamman tramadol, codeine da sauran kwayoyin magani masu sa maye.
Marwa ya gargadi cewa shaye-shaye ya kai matakin da zai iya rushe iyali kuma ya zama babban dalilin laifuka daga fashi da makami zuwa garkuwa da mutane da ta’addanci.
Maimakon raguwa, abubuwan da suka biyo baya sun nuna cewa matsalar ta kara tsanani.
A shekarar 2025, NDLEA ta sanya Kano a matsayin jiha ta biyu da ta fi kowace jiha yawan masu shaye-shaye a kasar.
A wannan shekarar ma, Kano Strategic Command ta kama mutane 1,389, ta kwace sama da tan 7.7 na kwayoyi, ta hukunta mutane 141, sannan ta wayar da kan sama da mutane 86,000.
Har zuwa tsakiyar 2026, hukumar ta lalata sama da tan 12 na kwayoyi da ta samu ta hanyar leken asiri, yayin da aka kama wasu daruruwan.
Wadannan lambobi suna nuna yadda ake kokari da kuma yadda cibiyoyin aikata laifi suka dage.
Shaye-shaye da laifuka sun zama abin da daya ke karfafa dayan. Burin samun kudin sayen kwaya kan tura wasu ga sata, kwacen waya da fashi.
‘Yan ta’adda ma suna amfani da jarabar son shan kwaya wajen shigar da matasa, karfafa masu laifi kafin su kai hari da kuma rike cibiyoyinsu.
Wadanda abin ya fi shafa su ne talakawa, su ake kwacewa waya a titi, a yi wa ‘yan kasuwa fashi, a kai wa matafiya hari, iyalai kuma na rayuwa cikin tsoro.
Matsalar ta wuce iya ta tsaro, duk matashin da ya fada cikin matsanancin ta’ammali da kwaya, asara ce ga ci gaban Kano.
Iyalai na kara talaucewa saboda kula da masu shaye-shaye, makarantu na fama da rashin tarbiyya, rashin kokari da rashin kwazo, Kasuwanci na wahala saboda rashin tsaro, masu zuba jari ma na tsoron zuwa.
Asibitoci suna kula da cututtukan da kwaya ke haddasawa, kotu kuma na cika da shari’o’in da suka shafi shaye-shaye.
Saboda haka shaye-shaye ba iya rayuwa kadai yake lalatawa ba, yana lalata ci gaban tattalin arziki da zamantakewar Jihar Kano.
Saboda haka kaddamar da wannan Kwamitin Aikin hadin gwiwa abin yabawa ne, ba kamar kokarin da ya gabata ba, wannan kwamitin ya hada hukumomi da ayyuka daban-daban ciki har da NDLEA, hukumomin tsaro da ma’aikatan gwamnati.
Ta jaddada bada bayanan sirri, hadin kai, gyara, wayar da kai da shigar al’umma, inda ta nuna cewa babu wata hukuma guda da za ta iya magance wannan matsala ita kadai.
Wani abin farin-cikin ma shi ne tabbacin da Shugaban Kwamitin, Barrista Muhuyi Magaji Rimingado ya bayar.
Ya ce kwamitin zai yi aiki ba tare da nuna bambanci ba kuma ba za a kyale ‘yan siyasa su shiga ba, wanda ya zama daya daga cikin manyan matsalolin tabbatar da bin doka a Najeriya.
Ya ce ba za a bari wani dan siyasa ko mai karfi ya fitar da wanda aka kama ba, wannan sako ne mai kyau a lokacin da mutane ke bukatar adalci daidai ga kowa.
Sai dai kalamai kadai ba za su magance matsalar ba.
Tabbatar da gaskiya yanzu na kan Gwamna Abba Kabir Yusuf, kafa kwamitin abu ne mai sauki amma tabbatar da nasararsa ne zai bukaci jajircewa, kudi da tsari.
Da farko, dole ne gwamnan ya tabbatar da ‘yancin kwamitin wajen aiki. Babu abin da ke raunata yarda da amincewar al’umma irin baiwa wasu fifiko a yayin aikin tabbatar da bin doka.
Na biyu, a baiwa kwamitin kayan aiki. Yaki da cibiyoyin miyagun kwayoyi na bukatar motoci, kayan sadarwa, leken asiri, kayan kariya, dakin bincike, kudi da jami’ai horayyu, kwamitin da ba shi da kayan aiki zai zama na ado kawai.
Na uku, gyara da saita masu shaye-shaye dole ne ya samu kulawa daidai da kama masu laifi, abu ne na kara gwiwa gwamnati ta yi alkawarin gyara, dawo da su cikin al’umma da ba su sana’a.
Wannan ya bambanta tsakanin ‘yan kasuwar kwaya da masu amfani da ke neman canji.
Ya kamata Kano ta kara cibiyoyin gyara, karfafa shawarwari, horon sana’o’i da bude kofa ga masu son komawa rayuwa mai amfani.
Ya kamata kwamitin ya kasu bangarori, leken asiri, aiki da tsare-tsare, shari’a, gyara, wayar da kai, hulda da al’umma da kuma tantance aiki, kowane bangare ya samu ayyuka da ma’auni.
Idan aka fitar da rahoto bayan kowane wata uku kan kama mutane, hukuntawa, gyara da kashe kudi, hakan zai tabbatar da amana.
Hulda da al’umma ma na da matukar muhimmanci, gwamnati kadai ba za ta iya ba. Iyaye su kula da ‘ya’yansu. makarantu su karfafa koyarwa kan hadarin kwaya. Malamai da sarakuna su yi wa’azi. Unguwanni su taimaka da bayanai. Kafafen yada labarai su yi yakin wayar da kai ba tare da cin zarafin wadanda ake son gyarawa ba.
Ya kamata gwamnatin Kano ta sanya wannan kwamitin cikin doka domin ya ci gaba ko da an samu sabuwar gwamnati.
Idan ba a sanya shi cikin doka ba, sauyin gwamnati na iya tafiya da shi.
Bawai iya yaki da kwaya kawai Kano ta ke ba, tana yaki ne domin tsaron al’umma, kariyar rayuka da dukiya, makomar matasa da ci gaba mai dorewa na daya daga cikin jihohi mafi muhimmanci a Najeriya.
Wannan shine yakin da gwamnati da kowane dan Kano bai kamata ya bari a bar shi a baya ba.













































