Gidauniyar Dr. Dahir Muhammad Hashim ta sanya yara daga iyalan da ke da karamin karfi 150 a makarantu daban-daban da ke fadin Karamar Hukumar Dala a Jihar Kano, a matsayin wani bangare na shirinta na tallafawa yara don komawa makaranta a shekarar karatu ta 2026/2027.
SolaceBase ta ruwaito cewa wannan shiri, wanda yanzu haka yake cikin shekara ta uku da farawa, na da nufin tallafawa yaran da iyayensu ke fuskantar wahalhalu wajen biyan bukatunsu na ilim, tare da tabbatar da cewa kalubalen kudi bai hana su samun ilimin matakin farko ba.
Su ma daliban da suka amfana da shirin, an samar musu da muhimman kayan karatu da suka hada da dinkin kayan makaranta, jakunkuna, littattafai da takalman, domin ba su damar komawa makaranta cikin shiri mai kyau domin sabuwar shekarar karatu.
An gudanar da taron ne a ranar Alhamis a Gidan Mumbayya da ke Gwammaja a Karamar Hukumar Dala, mai taken, “Sanya Hannun Jari a Fannin Ilimi don Gina Makoma Mai Kyau.”
Da yake jawabi a wurin taron, wanda ya kafa gidauniyar kuma Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi na Jihar Kano, Dr. Dahir Muhammad Hashim, ya bayyana cewa shirin ya fara ne shekaru uku da suka gabata a matsayin wani bangare na kokarin ba da gudummawa wajen gina al’ummar da tsararraki masu zuwa.













































