Gidajen mai za su rage farashin fetur nan kusa – IPMAN

IPMAN logo

Kungiyar masu sayar da man fetur masu zaman kansu ta kasa (IPMAN) ta bayyana cewa gidajen mai a fadin Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja, za su fara rage farashin fetur a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.

Sakataren yada labaran kungiyar na kasa, Chinedu Ukadike, ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a ranar Alhamis a Abuja.

Ukadike ya ce ‘yan kasuwa na shirin sauya farashinsu da dabarun sayar da mai da zaran sabbin kayayyaki sun shigo kasuwa.

Ya ce isowar sabbin kayayyakin na iya kawo sauye-sauye ga kasuwar a halin yanzu.

Ya kara da cewa ‘yan kasuwa za su yi gyare-gyaren da suka dace domin tabbatar da cewa masu amfani da man sun ci gaba da samun kayayyakin da suke bukata.

Ya ce lokacin isowar sabbin kayayyakin har yanzu ba a tantance shi ba, domin ‘yan kasuwa ba su riga sun sami tsayayyen kwanan wata ba.

A cewarsa, tsarin zai gudana ne karkashin dokoki da ka’idoji da ake da su.

“Daga zarar sabbin kayayyaki sun fara isowa, ana sa ran ‘yan kasuwa za su dauka da sauri ta hanyar duba farashinsu tare da sabunta kayayyakin da suke da su.

“Bayan wannan tsari, idan muka yi sayayya gobe ko jibi da zarar an fara, za mu daidaita farashinmu mu fara samar da sabbin kayayyakin ga masu amfani da su.

“Sayarwar na iya farawa a cikin ‘yan kwanaki kalilan, dangane da lokacin da aka fara tsarin a hukumance,” in ji shi.

Ya ce ana ran wannan ci gaban zai samar da sauye-sauye ga kasuwa yayin da gidajen mai ke daidaita farashinsu tare da samar da sabbin kayayyakin ga masu amfani da su.

Kamfanin Dillancin Labarai na NAN ya rawaito cewa matatar mai ta Dangote ta kara farashin mai daga matatar Naira 1,165 kan kowace lita zuwa Naira 1,185, sannan kuma zuwa Naira 1,200 da Naira 1,265 a cikin mako guda da ya gabata.
(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here