Dan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar NDC, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi Allah wadai da sabuwar barazanar hare-haren ‘yan bindiga da aka ruwaito a wasu sassan jihar, inda ya bukaci a dauki matakin tsaro cikin gaggawa da hadin kai domin kare al’ummomin da ke cikin hatsari.
Gwarzo, a cikin wata sanarwa da Kakakinsa, Ibrahim Garba Shuaibu, ya fitar a ranar Talata, ya nuna jimaminsa ga wadanda harin ya rutsa da su da iyalansu, musamman mazauna Chiromawa a Karamar Hukumar Garun Mallam, Beli a Karamar Hukumar Rogo, Bebeji da garuruwan da ke kewayen Gwarzo da harin ya shafa.
Ya bayyana hare-haren a matsayin barazana mai firgitarwa ga rayuwa, hanyoyin samun abinci da harkokin tattalin arziki, inda ya gargadi cewa kada a tilastawa mazauna yankin su bar gidajensu, gonakinsu da kasuwancinsu saboda ayyukan ‘yan ta’adda.
Dan takarar na NDC ya yi ta’aziyya ga iyalan da suka rasa ‘yan uwa, sannan ya nuna tausayawarsa ga wadanda suka jikkata, suka rasa matsuguni ko kuma suka shafu ta kowace hanya sakamakon harin.
Ya bukaci hukumomin tsaro da su kara karfafa tattara bayanan sirri, sa ido da gudanar da ayyuka na musamman a yankunan da ke cikin hatsari, tare da jaddada bukatar daukar mataki cikin sauri duk lokacin da aka gano wata barazana mai inganci.
Gwarzo ya kuma roki gwamnati da ta gano da kuma dakile hanyoyin tsaro don za su iya baiwa ‘yan bindiga, masu garkuwa da sauran kungiyoyin laifi damar kafa sansanoni a yankunan karkara.
A cewarsa, kare rayuka da dukiyoyi na daga cikin manyan ayyukan gwamnati kuma dole ne a dauke su a matsayin mafiya fifiko na gaggawa.
“Duk rayuwar da aka rasa sakamakon ta’addanci yana sosa zuciya, akwai bukatar daukar matakin gaggawa na karfafa tsarin tsaron mu. Bai kamata mu kyale al’ummarmu su zama fursunoni a cikin garuruwansu ba.
“Muna ta’aziyya ga iyalan da suka rasa ‘yan uwa kuma muna tare da duk wadanda wannan mummunan hari ya shafa. Gwamnati dole ne ta dauki mataki wajen kare rayuka, tsare al’ummomi da dawo da amincewar mutanen mu.”
Gwarzo ya yaba wa jami’an tsaro bisa kokarinsu na yaki da ‘yan ta’adda kuma ya bukaci su ci gaba da ayyukan da suka dogara da bayanan sirri tare da inganta tsarin amsa kiran gaggawa a yankunan da aka gano suna cikin hatsari.
Ya kuma roki mazauna yankunan da su kasance masu lura tare da ba wa hukumomin tsaro bayanai masu inganci, yana mai cewa bayanai a kan lokaci na iya taimakawa wajen hana hare-hare, ceto wadanda aka yi garkuwa da su kamawa da gurfanar da masu laifi.












































