Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf da takororinsa na jihohin Yobe, Sakkwato da Jigawa, sun jinjina wa Shugaban Majalisar Kungiyar Jama’atul Izalatul Bid’a Wa Iqamatussunnah (JIBWIS) na Kasa, Sheikh Sani Yahaya Jingir, saboda kokarinsa na dorewa wajen samar da hadin kai, zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin Musulmi da ma daukacin ‘yan Najeriya.
Bayani hakan na kunshe cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Talata.
Gwamnonin sun yi wannan jinjina 0ne a yayin babban taron tattaunawa na kasana kwana daya mai taken “Inganta Shiga Harkokin Siyasa da Goyon Bayan Adalci a Zamantakewa a matsayin Mafita ga Hadin Kai da Ci Gaban Najeriya,” wanda aka gudanar a dakin taro na Saddiqa Event Centre da ke Jos, a Jihar Plateau.
Taron ya kuma shafe wani gagarumin sauyi na siyasa, inda kungiyar JIBWIS ta yi kira ga mambobinta na fadin kasar nan da su marawa tare da zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Da yake jawabi a wurin taron, Shugaban Gudanarwar JIBWIS na Kasa, Sheikh Abdulnasir Abdulmuhuyi, ya nuna gamsuwarsa da gwamnatin Tinubu da Shettima, inda ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta nuna gaskiya da kwazo wajen ci gaban Najeriya a cikin shekaru uku na farko da ta shafe tana mulki.
Sheikh Abdulmuhuyi ya kara da cewa gwamnatin ta cancanci goyon bayan ‘yan Najeriya a karo na biyu domin ta kammala ayyukan da ta faro da kuma ci gaba da tsare-tsarenta na bunkasa kasa.
A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Ulaman JIBWIS na Kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya bukaci mambobin kungiyar a fadin kasar nan da su sabunta goyon bayansu ga Shugaba Tinubu da Mataimakin Shugaban Kasa Shettima gabanin zaben shugaban kasa na 2027.
Yayin da yake magana a madadin gwamnonin Kano, Sakkwato, Jigawa,da Yobe, Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya tuna da tarihin siyasar Najeriya, musamman zaben shugaban kasa na shekarar 1993 inda marigayi MKO Abiola ya tsaya takara tare da mataimaki Musulmi, wato Ambasada Babagana Kingibe.
Gwamna Buni ya yaba wa Sheikh Jingir saboda juriyarsa da sadaukarwarsa wajen samar da hadin kan kasa ta hanyar wa’azozinsa, yana mai bayyana kokarinsa a matsayin babban jigo wajen samar da zaman lafiya tsakanin ‘yan Najeriya.
A cikin sakonsa na fatan alheri, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya bayyana cewa ‘yan Najeriya ba za su iya jure wa rashin gwamnatin Tinubu da Shettima ba a shekarar 2027.
Sanata Barau ya kuma yaba wa Sheikh Jingir bisa kokarinsa na tabbatar da hadin kai da samar da zaman lafiya a fadin kasar nan.
A gefe guda kuma, Hon. Ibrahim Kabir Masari da Gwamna Mai Mala Buni kowannensu ya bayar da gudunmawar naira miliyan 300 domin gina Jami’ar Fortune, wacce Sheikh Sani Yahaya Jingir ya assasa.
Taron ya samu halartar fitattun malaman Musulunci, shugabannin siyasa, jami’an gwamnati da kuma mambobin JIBWIS daga sassa daban-daban na kasar nan domin tattaunawa kan shiga harkokin siyasa, adalci a zamantakewa, hadin kan kasa da kuma dorewar ci gaba a Najeriya.













































