Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta kori Farfesa Sani Lawan Malumfashi daga zama shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano, KANSIEC, bisa samunsa da laifin zama dan jam’iyyar siyasa.
SolaceBase ta ruwaito cewa Mai shari’a Simon Amobeda ya yanke hukuncin ne a ranar Talata, a karar da Aminu Aliyu Tiga da jam’iyyar APC suka shigar.