Tauraruwar fina-finan Kannywood, Nafisa Abdullahi ta bayyana cewa ba za ta kara fitowa a cikin shirin Hausa mai dogon zango da ake nunawa a tashar Arewa24 ‘Labarina’ ba.
Jarumar ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram a daren Asabar.
Nafisa ta ce ta ji dadin rawar da ta taka a shirin, amma ta ce ba za ta iya ci gaba da shi ba saboda wasu dalilai na kashin kai.
Nafisa Abdullahi dai ita ce jarumar da ta fi shahara a Google a shekarar 2021
Nafisa ta kasance babbar tauraruwa a shirin Labarina inda take fitowa a matsayin Sumayya.
Ga sanarwar da ta wallafa nan a ƙasa da harshen Turanci……