Wani bangon aji ya rushe tare da yin sanadiyar mutuwar daliba, da raunata wasu

mfd

Wata daliba mace ta mutu, yayin da wasu hudu suka samu raunuka bayan da bangon aji ya rufta a makarantar sakandaren mata ta gwamnati da ke Potiskum.

Dakta Bukar Bukar, babban sakatare na ma’aikatar ilimi a matakin farko da sakandare, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Alhamis a Potiskum.

Ya bayyana cewa dalibai 50 da ke makarantar babbar sakandare aji na biyu ne a rukunin ginin da ke da ajujuwa biyu.

“Wani sashe na shingen ajujuwa ya gangaro kan titin, kuma abin takaici, dalibanmu biyar abin ya shafa.

“Daya daga cikin su ta rasu, kuma hudu daga cikinsu suna samun kulawar likitoci a asibiti” in ji shi.

Bukar ya kara da cewa ma’aikatar tana jiran cikakken rahoto daga makarantar yayin da ma’aikatar gidaje ta kafa wani kwamiti da zai binciki musabbabin rugujewar ginin domin kaucewa sake faruwar lamarin.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa lamarin ya haifar da kaduwa da fargaba a tsakanin iyaye. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here