Kotu ta dakatar da jam’iyyu daga kawo tsaiko ga shirin zaben kananan hukumomi a Kano

Kano High Court

Wata babbar kotun jihar Kano karkashin mai shari’a Sunusi Ado Maaji, ta bayar da umarnin hana jam’iyyun APC, PDP, da wasu jam’iyyun siyasa 19, hana su kawo cikas ga karbar kudaden tsayawa takara a zaben kananan hukumomi da ke tafe wanda Hukumar KANSIEC ta sanar.

Da farko dai jam’iyyun siyasar sun ki amincewa da kudaden da KANSIEC ta kayyade, wadanda suka hada da Naira miliyan 10 na ‘yan takarar ciyamomi da kuma Naira miliyan 5 na ‘yan takarar kansiloli.

KANSIEC ta rage kudaden zuwa Naira miliyan 9 na ciyamomi da kuma Naira miliyan 4 na kansila biyo bayan magantuwa da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi.

A ranar 26 ga Oktoba, 2024 ne za a gudanar da zaben kananan hukumomi a Kano.

Wadanda ake tuhumar sun hada da Accord Party, Action Alliance, Action Democratic Party, African Democratic Congress, All Progressives Congress, Allied Peoples Movement, All Progressives Grand Alliance, Boot Party, Labour Party, National Rescue Movement, New Nigeria Peoples Party, Peoples Redemption.

Jam’iyya, Social Democratic Party, Young Progressive Party, Young Party, da Zenith Labour Party.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here