Garba Shehu ya warke daga Covid-19 

Garba Shehu1
Garba Shehu1

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya bayyana cewa ya warke daga cutar Covid-19.

Shehu, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebookk inda ya ce: “Ina godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya bani lafiya na murmure daga COVID-19.

Idan za a iya tunawa a ranar 25 ga Disamba, labarin manyan hadiman shugaban kasa da suka kamu da COVID-19, ya mamaye kafafen yada labarai.

Ma’aikatan sun hada da babban sakatare a fadar gwamnati, Tijjani Umar; Mataimaki ga shugaban kasa, ADC Yusuf Dodo; babban jami’in tsaronsa, Aliyu Musa, da babban mai taimaka masa na musamman kan kafofin yada labarai da yada labarai, Garba Shehu.

Yace “Ina kuma mika addu’a da girmamawata gare ku duka, waɗanda kuka yi addu’a, suka kira ko aika saƙonnin rubutu kuna bayyana damuwarku a gare ni. “Allah ya sa dukkan ‘yan kasarmu da ke fama da kwayar cutar su rabu da wannan annoba kuma su samu lafiya nan ba da jimawa ba.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here