Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano (MAKIA), Kano, sun kama wata mata mai suna Bilkisu Mohammed Bello, ‘yar shekara 45, dauke da kwalayen hodar iblis a lokacin da take shirin shiga jirgin saman Saudia zuwa kasar Saudiyya.
Wata sanarwa da Femi Babafemi, Daraktan Hukumar NDLEA, Media & Advocacy, ya fitar ranar Lahadi a Abuja, ta ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Talata.