Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan karar da Mawallafin PRNigeria ya shigar kan NIPSS

imgonline com ua twotoone Lq11XxARkRfH 750x340

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 19 ga Yuni domin yanke hukunci kan kar da Mawallafin PRNigeria, Yushau Shuaib, ya shigar, inda yake kalubalantar fitar da shi dagDarasin Babban Jami’i na 47 na Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabaru ta Kasa, NIPSS, Kuru-Jos.

Mai Shari’a Binta Nyako ce ta sanya ranar, a ranar Laraba bayan lauyoyin bangarorin biyu sun gabatar da hujjojin rubutu na goyon baya da na adawa da kara.

A yayin da ake ci gaba da sauraren karar, Lauyan Shuaib, Mista Teslim Adigun, ya shaida wa kotu cewa mai kar ya shigar da jingina mai kunshe da sakin layi 43, tare da shaidun gani da ido 14 da kuma hujjar rubutu na goyon bayan karar.

Adigun ya roki kotu da ta amince da bukatun wanda yake kare wa ta hanyar ayyana fitar da shi daga darasin a matsayin abin da ba bisa ka’ida ba da kuma umartar a sake mayar da shi cikin darasin.

Da yake mayar da martani, Lauyan NIPSS, Mista P. A Akubo, SAN, ya ce zargin mai kar an kambabashi ne, yana mai rokon kotu da ta watsar da kar.

Ya ce mai karar yana neman kotu ta ba shi diyya har Naira100 miliyan saboda cutarwa ta jiki da ta mutunci.

Mai karar yana kuma neman kotu ta haramta wa NIPSS ci gaba da nuna masa tsangwama ko tsoratarwa.

Bayan sauraren dukkan hujjoji, Mai Shari’a Nyako ta sanya ranar 19 ga Yuni domin yanke hukunci.

Tun da farko, alkaliyar ta umarci mai karar da ya mayar da makullen dakin kwanan daliban da ke hannunsa.

Mai karar ya ce yana rike da makullen ne bisa hujjar cewa kudi Naira 18.3 miliyan da ya biya na darasin sun hada da kudin masauki na tsawon lokacin darasin, kuma an ba shi dakin bisa wannan dalili.

Ya ce ba a dakatar da shigarsa cikin shirin bisa ka’ida ba, yana mai cewa dokar dakatarwa da fitar da shi daga darasin shi ita ce abin da yake rokon kotu tanke hukunci a kai. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here