Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Osun ta kama Kwamishinan Muhalli na jihar, Mayowa Adejoorin, bisa zargin harba bindiga da ya haddasa hargitsa a taron gangamin yakin neman zaben jam’iyyar APC a garin Ilesa a ranar Asabar.
Rahonni sun bayyana cewa lamarin ya yi sanadiyar jikkata mutane hudu, ciki har da wani yaro dan shekara 14 wanda aka ce harsashin kan mai uwa da babi ya same shi yana tsaye a shagon mahaifiyarsa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Osun, Abiodun Ojelabi, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun gano hujjoji da suka hada da kwanson harsashi da hular jami’an tsaro ta Amotekun bayan da aka killace wurin da lamarin ya faru.
“Labarin faruwar lamarin ya same mu, nan da nan jami’anmu suka garzaya wurin, suka killace yankin kafin aka gano wasu hujjoji, wadanda suka hada da kwanson harsasai da hulunan jami’an Amotekun,” in ji Ojelabi.
“Haka kuma, an kama Mista Adejoorin a daidai wurin da abin ya faru, kuma an tafi da shi hedkwatar rundunar domin yi masa tambayoyi a matsayin wani bangare na ka’idar bincike.”
‘Yan sandan sun ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin harbe-harben.
Sai dai kuma, kungiyar yakin neman zabe ta Imole Campaign Council, wadda ita ce kungiyar yakin neman zaben gwamnan jihar Ademola Adeleke, ta yi tir da kama kwamishinan, inda ta bayyana shi a matsayin matakin siyasa.
Yayin da yake jawabi a taron manema labarai a garin Osogbo, kakakin kungiyar, ya yi zargin cewa kamun na daya daga cikin manyan makircin tsoratar da shugabannin jam’iyyar Accord gabanin zaben gwamna.
“Wanda abin ya shafa na baya-bayan nan a cikin wannan salon abin damuwar shi ne mai girma kwamishinan muhalli, Hon. Mayowa Adejoorin,” in ji shi.
“Yadda aka kama shi abin damuwa ne kwarai da gaske. Muna kallon abin da ya faru da Hon. Adejoorin tamkar garkuwa da mutane irin ta ‘yan fashi da aka gudanar a karkashin inuwar hukumar ‘yan sanda.”
Olajengbesi ya yi zargin cewa an kama shugabannin jam’iyyar Accord da dama a yankin Ijesaland kwanan nan kan zarge-zargen da ya bayyana da cewa na siyasa ne.
Ya yi kira ga Sufeton Janar na Yan sanda (IGP), Tunji Disu, da ya shiga tsakani tare da bayar da umarnin sakin Adejoorin cikin gaggawa.
“Muna neman amsoshi kan dalilin kama Hon. Mayowa Adejoorin? Wane laifi ya yi? Wace hujja ce ke kansa?” ya tambaya.
Wannan takaddama dai na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da kungiyar yakin neman zabe ta Imole Campaign Council ta bukaci IGP da ya sauya wa Kwamishinan Yan sanda, Ibrahim Gotan, wurin aiki, wanda shi ke kula da tsaron zaben gwamnan jihar Osun na ranar 15 ga watan Agusta, bisa zargin cewa yana nuna bangaranci.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Bamidele Sallam, shugaban kwamitin yada labarai na kungiyar yakin neman zaben, ya zargi Gotan da taimakawa hare-haren da ‘yan bangar siyasa da ake zargin suna da alaka da APC ke kai wa magoya bayan jam’iyyar Accord.












































