Wani matashi mai yi wa kasa hidima (NYSC) da ke aiki a Jihar Kano ya nuna halin gaskiya da rikon amana ta hanyar mayar da kudi har naira 569,000 da aka tura a asusunsa na banki bisa kuskure.
Matashin, mai suna Jameelu Muhammad, dan rukunin farko na shekarar 2026 (Batch A, Stream II) wanda aka tura don yin aiki a Karamar Hukumar Kibiya ta jihar, ya sami sakon shigar kudin ne da ba ya tsammani a ranar 5 ga watan Agusta, 2026.
A cewar Jameelu, ya tashi da safe ne sai ya ga an tura naira 569,000 a cikin asusunsa na OPay, duk da cewa ba ya jiran wani kudi daga kowa.
Maimakon ya kashe kudin ko ya boye su, sai ya yanke shawarar binciko asalin inda kudin suka fito domin tabbatar da cewa sun koma hannun ainihin mai su.
Yayin da yake zantawa da SolaceBase a ranar Asabar, Jameelu ya ce samun sakon kudin ya firgita shi da farko, amma da sauri ya fahimci cewa rike kudin zai jefa mai su cikin tsananin damuwa da kunci.
“Na firgita sosai saboda ba na tsammanin irin wannan makudan kudi daga ko’ina. Yayin da zuciyata ta soma bugawa da sauri, sai na dakata na yi tunani, na tambayi kaina idan na yanke shawarar rike wadannan kudi, wane irin halin matsin lamba mai su zai shiga?” in ji shi.
Ya kara da cewa shawarar da ya yanke ta dace da kyawawan dabi’u na gaskiya da rikon amana da ake tsammani daga jami’an NYSC dake yi wa kasa hidima.
Rahonni sun bayyana cewa mamallakin kudin, mai suna Shamsu Usman, ya tura kudin ne bisa kuskure sa’ilin da yake kokarin aika kudi.
Bayan an gano asalin kudin kuma an mayar masa, Usman ya nuna matukar godiyarsa ga Jameelu saboda nuna gaskiya da rikon amana.
Wannan mataki na gari ya sami yabo mai yawa a karamar hukumar Kibiya da ma sauran sassa, inda aka bayyana halin matashin a matsayin misali na gari na zama dan kasa nagari, kishin kasa da kuma sadaukarwa.












































