Majalisar Dokokin kebbi tayi sammacin Gwamnan Jihar

images 12 3 697x430 1
images 12 3 697x430 1

Majalisar dokokin jihar Kebbi ta gayyaci gwamnan jihar, Abubakar Atiku Bagudu kan amfani da bashin Nera Milyan Dubu 18.7 daga gwamnatin tarayya.

A cikin wasikar da majalisar ta aikewa gwamnan mai kwanan wata 26 ga watan Janairu, 2023 da solacebase ta gani, majalisar ta bukaci gwamnan ya bayyana a gabanta a ranar Juma’a 27 ga watan Janairu, 2023.

A cewar wasikar hakan ya yi daidai da kokarin da majalisar ta yi na tabbatar da kula da dukiyar jihar cikin tsanaki .

Wasikar ta kasance kamar haka: Dangane da bukatar ku na amincewa da Gwamnatin Kebbi ta karbo bashin kudi daga gwamnatin tarayya mai kwanan wata 18 ga Oktoba, 2021 tare da mai lamba No. GHBK/8/21 Vol.1

‘’ Majalisar Dokokin Jihar Kebbi ta amince da kudi har sama da Naira Miliyan Dubu Goma sha Takwas (18,746, 059,992.57) ta hanyar kudiri mai kwanan wata 18 ga Oktoba, 2021.’’

A ci gaba da kokarin da take yi na kula da albarkatun kasa cikin tsanaki majalisar tana neman Gwamnan da ya gurfana a gaban majalisar domin yin bayani kan yadda za ayi amfani da kudaden a ranar Juma’a 27 ga Janairu, 2023 da karfe 10:00 na safe.

Jaridar solacebase ta rawaito cewa wasikar da Suleiman Shamaki, mukaddashin magatakardar majalisar ya sanyawa hannu tana mai take ‘’Re: Offer of Federal Loan Facility’’.

An makala wasikar ne tare da sanya hannun ‘yan majalisa 20 daga cikin 24 na majalisar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here