Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC ta bukaci babban bankin Najeriya CBN da ya kara wa’adin ranar 31 ga watan Janairu domin kawar da tsofaffin takardun kudi a kasar nan.
Shugaban kungiyar Mista Ayuba Wabba ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan nasarorin da ya samu da kalubalen da ya fuskanta a matsayinsa na shugaban kungiyar na tsawon shekaru takwas.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya rawaito cewa Wabba, wanda aka zaba a matsayin shugaban kungiyar na kasa a shekarar 2015, ya yi wa’adi biyu.
Wabba ya ce umarnin da majalisar dattawa ta bayar na neman a kara wa’adin abune da ya dace.
Ya ce hakan ya biyo bayan yadda akasarin ‘yan Najeriya da ke zaune a lungu da sako na kasar da babu bankuna har yanzu ba su samu damar sauya tsaffi da sabon kudin Naira ba.
A cewarsa, a matsayinmu na NLC, “mun yi kokarin mayar da martani a hukumance ta hanyar rubutawa gwamnan CBN. Mun kuma rubuta wa shugaban kasa cewa, wannan sabuwar manufar ta sauya Naira tana bukatar a sake duba ta.
“A bayyane yake cewa ko a cikin manyan biranen, bankuna suna ba da tsofaffin takardun kudi kuma wannan daidai ne. Na je kusan bankuna 10 kuma babu wanda ke rarraba sabbin kudin.
“Don haka ba a samu sabbin takardun ba kuma ba sa yaduwa kuma ana watsi da tsoffin takardun.
“Idan ka je yankunan karkara ka ga yanayin rudani na yadda mutane suka zo da kudadensu suna canjawa, ya zama matsala,” inji shi.
Don haka shugaban NLC ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta duba lamarin a tsanake kafin a kai nutsar da tsaffin kudin a cikin bankuna a kasar nan.
Wabba ya ce dole ne gwamnati ta yi tunani ta hanyar fito da sabbin manufofin Naira domin kada jama’a su fuskanci illar wannan manufa.











































