Kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na jihar Kano, Dakta Dahir M. Hashim, ya kaddamar da sabbin babura masu amfani da wutar lantarki da aka ƙera domin jigilar amfanin gona cikin sauƙi da kare muhalli daga gurbata.
An gudanar da taron kaddamarwar a ranar Alhamis a cibiyar Mata Zalla Smart Agro-Cargo Base Station da ke ƙaramar hukumar Kura ta jihar Kano.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa wannan shiri na zamani an aiwatar da shi ne ta ƙungiyar masu kananan sana’o’i ta Mata Zallah tare da tallafin Prompcom+, ƙarƙashin ofishin ma’aikatar harkokin waje, da harkokin dauloli da ci gaban ƙasashen waje ta Biritaniya (FCDO).
Dakta Hashim ya bayyana cewa wannan shiri muhimmin mataki ne wajen ƙarfafa tattalin arzikin mata da tabbatar da ci gaba mai ɗorewa da kare muhalli a jihar Kano.
Karanta: Kano ta kori wasu jami’an shari’a bisa rashin Ɗa’a, ta ladabtar da wasu
Ya ce amfani da baburan lantarki zai taimaka wajen ƙara yawan shigar mata a harkar kasuwancin noma, rage ɓarnar amfanin gona bayan girbi, da rage fitar da hayaƙin da ke gurbata muhalli.
Kwamishinan ya yaba wa ƙungiyar Mata Zallah bisa jajircewarsu wajen inganta rayuwar mata, tare da tabbatar musu da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa musu domin dorewar wannan shiri.
Ya kuma bayyana cewa wannan aikin ya yi daidai da hangen nesa na Gwamna Abba Kabir Yusuf na ƙarfafa mata da gina Kano mai tsafta, kore, da ci gaba.













































