Hukumar kula da ayyukan shari’a ta jihar Kano ta ɗauki matakan ladabtarwa kan wasu jami’an shari’a da ma’aikata bisa aikata laifukan rashin da’a daban-daban, tare da yabawa wani alkali bisa gaskiya da ƙwarewa a aikinsa.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar shari’a ta jihar, Baba Jibo Ibrahim, ya sanya wa hannu, hukumar ta bayyana cewa ta yanke waɗannan hukunci ne a zama na 86 da ta gudanar a ranar 30 ga Oktoba, 2025, bayan ta karɓi shawarwarin kwamitin korafe-korafe da bincike na shari’a (JPCC) wanda ya binciki koke-koke da ƙorafe-ƙorafe kan jami’an kotuna da ma’aikata.
Sanarwar ta bayyana cewa Isa Yuguda Wudilawa, babban rajistara a kotun majistare da ke Zungeru, an same shi da laifin karɓar kuɗin gwamnati a cikin asusun kansa don wasu ayyukan hukuma, wanda ya saba wa ƙa’idojin gudanar da kuɗi da ɗabi’ar aikin gwamnati.
Hukumar ta sauke shi daga matakin aiki na 12 zuwa 10 bisa tanadin sashe na 04305 na dokokin ma’aikatan jihar Kano da tanadin 41(d) na ƙa’idar hukumar shari’a ta jihar, 1980.
Alkali Ibrahim Isah Usman na kotun shari’a ta Bebeji ya yanke hukunci kafin cikar kwanaki talatin da doka ta tanada don daukaka ƙara.
Hukumar ta yi masa gargaɗi mai tsanani tare da dakatar da ci gaban matsayinsa na shekara guda.
Har ila yau, Alkali Shamsu Maul’ainaini na kotun shari’a ta Durbunde an same shi da laifin yin ba daidai ba wajen kuɗaɗe da sauran halaye marasa kyau.
Hukumar ta amince da shawarwarin kwamitin binciken, ta sauke shi daga matsayinsa zuwa na rajistara tare da gargaɗi mai tsanani saboda cire takardun kotu da yin aiki da ya sabawa umarnin zagaye na 2 na shekarar 2021.
Hukumar ta kuma kori Ibrahim Salim, magatakarda a kotun shari’a ta Rijiyar Lemo, bayan an same shi da laifin yin jabun takardu, canza bayanan kotu, da karɓar rashawa daga masu shari’a.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa hukumar ta yaba da gaskiya da ƙarfin gwiwar Alkali Ali Jibrin Danzaki na kotun shari’a ta Rijiyar Lemo saboda fallasa munanan ayyukan magatakardansa, inda aka ba shi takardar yabo bisa abin koyi.
Haka kuma, hukumar ta ce Alkali Munzali Tanko (mai ritaya) wanda tsohon alkalin kotun shari’a ta Post Office ne, ya ci gaba da gudanar da shari’a bayan ya yi ritaya tsawon kwanaki tara.
Hukumar ta bayyana hakan a matsayin abin kunya da rashin gaskiya, ta kuma umurci a bayyana laifinsa domin zama izina ga wasu.
A wani lamari daban, alkaliya Halima A. B. Wali ta samu gargaɗi mai tsanani bayan ta kasa bin tsarin doka a shari’ar Kwamishinan ‘yan sanda da Ashiru Me’wushirya.
Haka kuma, Alkali Abdul’aziz M. Habib an same shi da yin shari’o’i ba tare da bin umarnin hukuma ba.
Duk da haka, hukumar ta yi la’akari da nadamarsa, ta rage masa albashi zuwa rabin kuɗi na tsawon watanni uku tare da gargaɗi.
Hukumar ta jaddada kudirinta na tabbatar da ladabi, gaskiya da bin ka’idoji a fannin shari’a, tana mai gargadi cewa duk wanda aka samu da aikata rashin da’a zai fuskanci hukunci mai tsanani.













































