Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da gina sabbin gidaje na gwamnati ga shugabannin manyan kotunan tarayya, tare da amincewa da ayyukan samar da ruwa da sauran ayyukan gina ababen more rayuwa a babban birnin tarayya Abuja.
Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ne ya bayyana haka bayan taron majalisar zartarwa da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya jagoranta a fadar gwamnati da ke Abuja.
Wike ya bayyana cewa amincewar ta shafi ƙirƙira da gina gidajen zama na gwamnati ga shugabannin kotunan daukaka ƙara, shugabannin kotunan masana’antu, babban alkalin kotun tarayya, da babban alkalin kotun babban birnin tarayya.
Ya ce aikin ya riga ya fara kuma an shirya haɗin gwiwa tsakanin kwararru don tabbatar da an kammala shi cikin lokaci.
Haka kuma majalisar ta amince da sabbin ayyukan samar da ruwa da za su rika samar da ruwa ga garuruwan Karu, Karshi, Orozo da Bwari a yankunan karkarar babban birnin tarayya.
Wike ya tuna cewa shugaban ƙasa ya kaddamar da wani ɓangare na aikin samar da ruwa na babban Abuja a baya, wanda yanzu za a faɗaɗa zuwa waɗannan yankuna.
Ministan ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da aikin gyaran cibiyar taron kasa da kasa ta Bola Ahmad Tinubu wacce aka fara gyarawa ta gaggawa don ta dace da ƙa’idodin ƙasa da ƙasa kafin taron majalisar ƙasashen yankin ECOWAS da aka yi a baya.
An kuma amince da sabuwar kwangila don aikin gina ababen more rayuwa a unguwar Maitama II da ke babban birnin tarayya, bayan soke tsohuwar kwangilar da ba ta fara aiki ba tsawon shekaru biyar.
Wike ya bayyana cewa aikin Maitama II zai shafi fili mai faɗin sama da eka 786, inda yawancin filayen tuni aka raba su ba tare da an gina hanyoyi ko sauran muhimman abubuwa ba.
Ya ce wannan aiki babban shiri ne da gwamnati za ta mai da hankali sosai don buɗe sabon yankin da inganta ci gaban sa.











































