Gwamnatin Tarayya ta dakatar da sayar da kadarorin hukumar filayen jiragen sama ta ƙasa, yayin da Majalisar zartarwa ta amince da gudanar da harkokin haya

FAAN Logo

Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin dakatar da sayarwa ko musayar kadarorin hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya da ke cikin da wajen filayen jiragen sama, tana mai jaddada cewa duk waɗannan kadarorin na musamman ne don amfanin harkar sufurin jiragen sama.

Gwamnatin ta kuma gargadi ƙungiyoyin ma’aikata da ke filayen jiragen sama da su guji tsoma baki a cikin manufofin gwamnati, tare da tabbatar da cewa shirin yarjejeniyar haya na filayen da ba su da riba ba zai jawo asarar ayyukan ma’aikata ba.

Ministan harkokin jiragen sama da ci gaban sararin samaniya, Festus Keyamo, ne ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya jagoranta a fadar gwamnati da ke Abuja.

Keyamo ya bayyana cewa wannan umarni ya shafi duk wasu fassarori na tsofaffin shirye-shiryen sayar da kadarori da aka yi a baya, yana mai cewa kadarorin hukumar FAAN kadarori ne na ƙasa masu muhimmanci da dole su ci gaba da kasancewa ƙarƙashin ikon gwamnati.

Ya ƙara da cewa ma’aikata masu muhimmanci kamar masu kashe gobara da jami’an kula da hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama dole ne su zauna a cikin yankin filayen don bada amsa cikin gaggawa a lokutan haɗari, don haka wajibi ne a riƙe waɗannan kadarori.

Majalisar zartarwa ta amince da buƙatun ma’aikatar jiragen sama guda takwas da suka shafi tsaro, sabunta fasaha, yarjejeniyar haya da kuma ƙarfafa tsaron filayen jiragen sama.

Hakan ya haɗa da gyare-gyare da kulawa ga tsarin bayanan zirga-zirga na jiragen sama a manyan filayen jiragen sama guda biyar — Abuja, Legas, Kano, Fatakwal da Enugu.

Haka kuma, majalisar ta amince da amfani da tsarin sadarwa na zamani (TETRA) da kuma kayan sadarwa na VHF guda 14 domin inganta tsaron zirga-zirgar jirage ta hukumar kula da sararin samaniya ta Najeriya (NAMA).

Ta kuma amince da siyan motocin kashe gobara guda 15 don filayen jiragen sama na ƙasa baki ɗaya domin cika ƙa’idojin ƙungiyar sufurin jiragen sama ta duniya (ICAO).

Bugu da ƙari, an amince da gina sabuwar cibiyar NAMA a Abuja domin kawar da haɗarin tsaro da ke tattare da aiki a cikin gine-ginen haya, tare da amincewa da shirin yarjejeniyar haya na filin jirgin sama na Fatakwal, wanda yanzu masu zuba jari da dama ke neman shiga ciki.

Majalisar ta kuma amince da shirin tantance fasinjoji ta hanyar na’urar tantamce yatsu da kuma haɗa bayanai da lambar shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) domin yaƙar amfani da sunaye na ƙarya da kuma inganta tsaro a filayen jiragen sama.

An amince da kwangilolin saka fitilu a wasu filayen jiragen sama domin su ci gaba da aiki har zuwa ƙarshen dare, lamarin da zai taimaka wajen ƙara samun kuɗaɗen shiga ga kamfanonin jiragen sama.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here