UTME: Hukumar JAMB ta gargadi masu yin jarrabawa da su kula da shafukan boge

JAMB, UTME, gargadi, jarrabawa, dalibai, yanar gizo, boge
Hukumar JAMB da ‘yan sanda sun gargadi masu jarrabawa da ke shirye-shiryen jarrabawar gama-gari ta 2024 (UTME) da su kula da shiga shafukan yanar gizo na...

Hukumar JAMB da ‘yan sanda sun gargadi masu jarrabawa da ke shirye-shiryen jarrabawar gama-gari ta 2024 (UTME) da su kula da shiga shafukan yanar gizo na bogi.

Hukumomin biyu sun yi wannan gargadin ne a wani taron manema labarai na hadin gwiwa a Abuja ranar Asabar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya ce akwai wasu shafukan yanar gizo na bogi da wasu marasa gaskiya suka kirkira da nufin yaudarar masu yin jarrabawa.

Karin labari: Sojoji sun kama mutane 6 masu sayar da kayan aikin Boko Haram a Borno

Ya kuma bukaci masu yin jarrabawar da su yi taka-tsan-tsan da dabarunsu, inda ya ce, an tsara yanar gizo na jabu ne domin yaudarar dalibai da ba su ji ba su gani ba, wajen ba da bayanan sirri kamar lambobin rajista da adireshin imel da kuma lambobin waya.

“Hukumar JAMB da rundunar ‘yan sandan Najeriya sun yi Allah-wadai da wadannan ayyukan damfara tare da sake jaddada shirye-shiryen kare muradun dalibai da kuma kiyaye sahihancin tsarin jarrabawar.

“Muna kira ga iyaye da masu kulawa da duk masu ruwa da tsaki da su tabbatar da cewa dalibai sun bi sanarwar da UTME ta tsara daga yanar gizo da hukumar ta amince da su kammar yadda aka gani kamar haka: www.jamb.gov.ng.”

Karin labari: Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya su hada kansu don ciyar da kasar gaba

Adejobi ya bayyana cewa rundunar ta san dabarun da ’yan damfara ke bi, musamman a lokacin tantancewar da kuma bayar da horo na shekara-shekara.

Don haka ya ce kungiyoyin biyu suna wayar da kan masu jarrabawar da jama’a game da wadannan dabi’u na yaudara.

“Duk dalibin da ya ziyarci wadannan shafuka na bogi ba shakka zai samu bayanan da ba za su iya dogaro da su ba kuma ta haka ne ya fadi a jarrabawar da ke tafe.

“An shawarci masu yin jarrabawar da su buga Slip Notification na UTME kafin ranar Juma’a, 19 ga watan Afrilun 2024, don samun muhimman bayanai game da jarabawarsu.

Karin labari: Sarkin Musulmi ya bukaci al’umma su nemi Ilimi tare da yiwa shugabanni addu’a

“Duk wani gidan yanar gizo ban da www.jamb.gov.ng da ke ba da sabis na bugu na UTME na bogi ne kuma an tsara shi don damfarar masu yin jarrabawa,” in ji shi.

Ya kuma yi kira ga masu yin jarrabwar da su yi hattara da gidajen yanar gizo da ke ba da tambayoyi da amsa ‘kai tsaye’, domin karya ne da yaudara, yana mai cewa an hana shiga irin wadannan waje.

Ya kuma jaddada cewa, Sufeto Janar na ‘yan sanda ya umarci hukumar NPF-NCCC da ta bi diddigin ‘yan damfara da masu damfara wadanda ke aikata laifukan da suka shafi yanar gizo tare da kirkiro shafukan yanar gizo.

Karin labari: Kotu ta saka ranar gurfanar da tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da matarsa ​​da wasu mutum 6

A nasa bangaren, kakakin hukumar ta JAMB, Dakta Fabian Benjamin, ya yi alkawarin hukumar na ci gaba da gudanar da ayyukanta.

Don haka ya bukaci masu jarrabawar da su yi watsi da duk wani sako da ba a so ba tare da lura da cewa sun fito ne daga abubuwan da ke da nufin damfarar dalibai ba.

Jarrabawar dai ta 2024 UTME an shirya farata ne a ranar Juma’a, 19 ga watan Afrilu, kuma a kammala a ranar 29 ga watan Afrilu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here