Rashin Tsaro: Wasu matafiya sun koka kan satar mutane a manyan hanyoyi

Rashin tsaro, manyan, hanya, Enugu, Ebonyi, matafiya, satar mutane
Wasu masu bin manyan hanyoyi a Ebonyi sun koka kan yadda ake zargin sace mutane a kan titin Idodo na babbar hanyar Enugu zuwa Abakaliki. Sun bayyana lamarin...

Wasu masu bin manyan hanyoyi a Ebonyi sun koka kan yadda ake zargin sace mutane a kan titin Idodo na babbar hanyar Enugu zuwa Abakaliki.

Sun bayyana lamarin a matsayin abin damuwa, sun kuma yi kira ga gwamnatin tarayya, Ebonyi da kuma gwamnatin Enugu da su shiga tsakani domin tabbatar da tsaro a babbar hanyar.

An dai samu takun saka a tsakanin matafiya da masu safara a Abakaliki, babban birnin Ebonyi, wadanda suke bin hanyar domin lamarin na barazana ga bil’adama.

Karin labari: UTME: Hukumar JAMB ta gargadi masu yin jarrabawa da su kula da shafukan boge

Garkuwa dai ya zama sana’a ga wasu a fadin jihohin tarayyar Najeriya, saboda yadda ake yawan sace mutane don neman kudin fansa ko tsafi.

Jerry Okonkwo, wani direban kasuwanci ne a ranar Asabar, ya bayyana damuwarsa kan lamarin kuma ya bayyana cewa yana tsoron kada a sace shi.

Okonkwo ya ce akwai bukatar gwamnati ta sa baki a kan manyan hanyoyin kasar nan.

Karin labari: Sojoji sun kama mutane 6 masu sayar da kayan aikin Boko Haram a Borno

“Abin takaici ne matuka yadda masu garkuwa da mutane ke bin hanyoyin kasar. Tsaron manyan tituna ya zama dole domin ci gaban kasa.

“Dan’uwana, ina matukar tsoron kada a yi garkuwa da ni saboda zan shafe watanni a kogon masu garkuwa da mutane saboda ba ni da wanda zai biya kudin fansa domin a sake ni.

“To, batun shi ne, ba zan iya daina tuki ba, domin ba ni da wata sana’a. Wannan shi ne abin da nake yi don samun abin rayuwa.

Karin labari: Sarkin Musulmi ya bukaci al’umma su nemi Ilimi tare da yiwa shugabanni addu’a

Lamarin da ake yi na sace mutane a kan hanyar wucewa abin damuwa ne,” ya kara da cewa.

Wani direba, Mista Ukeni Mathew, ya yi kira da a samar da ingantaccen hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin Ebonyi da Enugu domin dakile wannan mataki.

“Ina rokon ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro su tashi tsaye don shawo kan lamarin,” in ji shi.

Karin labari: Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya su hada kansu don ciyar da kasar gaba

Wata matafiya, Misis Margaret Uka, ta ce yin tafiya ta Abakaliki-Enugu ba ta da kyau, tana mai kira ga gwamnatoci su sa baki cikin gaggawa.

Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi DSP Joshua Ukandu, ya bayyana cewa sun dade da samun labarin halin da ake ciki a hanyar, amma kasancewar bangaren baya karkashin hukumar shiyasa suka yi burus da lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here