Tinubu Ya Isa Kasar Saudiyya Domin Taron Hadin Kan Kasashen Larabawa Da Musulunci

1731233490654

Shugaba Bola Tinubu ya isa birnin Riyadh na kasar Saudiyya, domin halartar taron hadin gwiwa tsakanin kasashen Larabawa da Musulunci da za a yi, wanda zai tattauna batutuwan da suka shafi yankin Gabas ta Tsakiya, musamman rikicin Isra’ila da Falasdinu.

Mataimakin Gwamnan Riyadh, Yarima Mohammed bin Abdulrahman ne ya tarbi Shugaba Tinubu a lokacin da ya isa.

Taron wanda aka shirya zai fara a ranar Litinin 11 ga Nuwamba, 2024, ana gudanar da shi ne bisa gayyatar Sarki Salman da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here