Ramadan: KAROTA ta fitar da wasu ka’idojin tuki lokacin Azumi 

KAROTA New 750x430

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta bukaci masu amfani da hanya musamman direbobi da su kasance masu hakuri da yin tuki a cikin natsuwa a watan Ramadan.

A cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na KAROTA, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa ya fitar a ranar Alhamis din nan, ya ce watan Ramadan lokacin ibada ne da ke kawo sauye-sauyen halayen tuki sakamakon kasala, rashin wadataccen ruwa a jiki, da yawan cunkoson ababen hawa, musamman a lokutan buda baki da tarawihi.

SolaceBase ta ruwaito cewa sanarwar ta ce domin tabbatar da tsaron lafiyar kowa da kowa a kan tituna, KAROTA ta shawarci direbobi da su bi wadannan ka’idoji a cikin watan Ramadan:

Karin karatu: KAROTA ta kama jabun magungunan kashe qwari da kuma magungunan da wa’addin amfani da su ya kare na sama da miliyan 30

A guji yawan Gudu kafin buda baki – Wasu direbobin kan garzaya gida domin yin buda baki, abin da ke haifar da cunkoson ababen hawa da hadurra, don haka dirbobi su i tuƙi a cikin aminci don kare kansu da sauran jama’a.

Kasance cikin Fadakarwa da Natsuwa – Azumi na iya haifar da gajiya ko juwa, a don haka KAROTA ta shawarci direbobi idan sun ji gajiya ko barci, u huta kafin ku ci gaba da tafiya.

Yin Haƙuri da Ladabi akan Hanya – Cunkoson ababen hawa na ƙaruwa, musamman a kusa da kasuwanni da masallatai. Direbobi su gujewa tuƙi da ganganci kuma nuna ƙosawa da rashin fahimta ga wasu.

Yawaita shan ruwa da cin abinci mara nauyi kafin Tuƙi – Tabbatar sa cewa direbobi sun sha isasshen ruwa kuma sun ci abinci mai sauƙi a lokacin Suhoor don kula da kuzari da mayar da hankali yayin tuki.

Kula da masu tafiya a ƙasa da masu keke – Mutane da yawa suna tafiya zuwa masallatai, musamman da dare. Direbobi su yi tuƙi a hankali, musamman a wuraren cunkoso.

Shirya shiryen fita a kan lokaci – Idan zai yiwu, ku guje wa tafiya a lokutan cunkoso da yawa kuma ku tuƙi lokacin da kuke cikin yanayi mai kyau.

Bin dokokin tafiya da amfani da umurnin jami’an KAROTA – Direbobi su kasance sun yi gudu daidai yadda aka umarta, tare da bin dokokin zirga-zirga don kare rayuwar su da ta wasu.

A cewar KAROTA za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaron tituna a cikin watan Ramadan kuma za ta kara yawan sintiri domin saukaka zirga-zirgar ababen hawa.

A don haka ta yi kira ga dukkan direbobi su rungumi hakuri, su mutunta juna, su yi tukin nutuswa a cikin wannan wata mai alfarma.

Shugaban hukumar KAROTA Faisal Mahmud Kabir yana yiwa kowa da kowa fatan alkairi da kuma fatan Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here