Babu daga kafa a yakin da ake yi da miyagun kwayoyi a Kano – Muhuyi

IMG 20260802 WA0487 750x430

Shugaban Hukumar Hadin Gwiwa ta Jihar Kano kan Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, Alhaji Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana cewa ba za a kyale kowa ba a yakin da ake yi da shaye-shaye da fataucin miyagun kwayoyi a jihar, inda ya yi gargadin cewa duk wanda aka kama da hannu a wannan haramtacciyar sana’a zai fuskanci cikakken fushin doka.

Yayin da yake jawabi a cikin wani shirin wayar tarho na “Duniyar Mu a Yau” a gidan rediyon Freedom Radio da ke Kano, Alhaji Muhuyi ya bayyana cewa tuni hukumar ta kai wasu majiyyata da ke fama da matsalolin shaye-shaye zuwa Cibiyar Gyaran Halayya ta Kiru a matsayin wani bangare na kokarin gyara rayuwar wadanda abin ya shafa da mayar da su mutane masu amfani ga al’umma.

Wata sanarwa da Lamara Garba, mamba a kwamitin yada labarai na hukumar ya fitar ranar Talata, ya ce shugaban ya kuma bayyana cewa an riga an gurfanar da da dama daga cikin wadanda ake zargi a gaban kotu saboda laifuka da suka shafi kwayoyi. Haka kuma an rufe shagunan sayar da magunguna da dama saboda keta dokokin da ke kula da sayarwa, sarrafawa da kuma adana magunguna.

A cewarsa, hukumar ba za ta kyale kowane mutum ko kasuwanci da aka samu yana saba wa ka’idojin da aka kafa ba, inda ya jaddada cewa za a aiwatar da doka ba tare da tsoro ko nuna bangaranci ba.

Ya gargadi masu safarar kwayoyi a fadin jihar da su gaggauta barin wannan harka ta barna, idan ba haka ba kuma za su fuskanci kamawa da hukunci.

“Ba za a saurarawa kowa ba. Duk wanda ya tsoma hannu a sayarwa ko shaye-shayen kwayoyi tabbas za a kama shi kuma a hukunta shi. Ba za a sami wurin boye irin wadannan masu laifi ba a Jihar Kano,” in ji shi.

Shugaban ya ce hukumar za ta fadada hadin gwiwarta da muhimman bangarorin al’umma, da suka hada da malamai, sarakunan gargajiya, kungiyoyin farar hula, kungiyoyin ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki, a matsayin wani bangare na tsari na bai-daya don fuskantar wannan annoba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here