’Yan Bindiga Sun Kashe Farfesan Jami’ar Ibadan

farfesa Opeyemi Isaac Ajewale
farfesa Opeyemi Isaac Ajewale

Wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun bindige wani malamin Jami’ar Ibadan, Farfesa Opeyemi Isaac Ajewole.

’Yan bindigar sun yi wa marigayin kwanton bauna ne a kan hanyarsa ta komawa gida a Moniya da ke kusa da birnin Ibadan.

Maharan sun kuma yi awon gaba da motar da yake tukawa bayan sun bindige shi.

Tuni dai rahotanni suka ce an kai gawar marigayin wajen ajiye gawarwaki na Jami’ar Ibadan.

Marigayi Farfesan, mai shekara 61 malami ne a Sashen Alkinta Dazuka na Jami’ar ta Ibadan.

Wani abokinsa mai suna Olukayode Ogunsanwo ya ce, “Abokina ne kuma gaskiya ne an kashe shi a jiya da dare a kan hanyar komawa gida. Sun harbe shi kuma sun tafi da motarsa”.

Mataimakiyar Rajistarar Makarantar a sashen sadarwa na Jami’ar,  Joke Akinpelu ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce, “gaskiya ne an bindige shi sai dai ba mu tabbatar cewa an yi hayar su aikata hakan ne ko ’yan fashi da makami ba ne.”

(Aminiya)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here