Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a, 12 ga Yunin 2026, a matsayin ranar hutu domin murnar bikin Ranar Dimokuradiyya ta wannan shekara.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da Babban Sakatare a Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Magdalene Ajani ta fitar a ranar Alhamis.
Ya ce murnar tunawa da ranar 12 ga Yuni na kowace shekara na da muhimmanci sosai a tsarin dimokuradiyyar Najeriya, inda ake tunawa da karfin gwiwa, juriya da sadaukarwar da ‘yan Najeriya da suka yi da gwagwarmaya don tabbatar da dimokuradiyya a kasar.
Tunji-Ojo ya sake jaddada kudurin Gwamnatin Tarayya na tabbatar da ka’idojin dimokuradiyya, ciki har da bin doka, gaskiya, alkinta dukiyar kasa da gwamnatin da za ta yi aiki da kowa.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati na ci gaba da kuduri don karewa da karfafa tsarin dimokuradiyya bisa ga alhakin da kundin tsarin mulki ya dura mata.
Ministan ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida tare da hadin gwiwa da jami’an tsaro da suka dace, za su ci gaba da karfafa matakan tsaron cikin gida domin kare rayuka da al-umma a fadin kasar.
Ya jaddada cewa zaman lafiya da tsaro na da matukar muhimmanci wajen kare dimokuradiyya da inganta cigaban kasa.
Ya kuma roki ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan dama wajen tunani, Tunji-Ojo ya bukaci ‘yan kasa su sake sada kansu wajen tabbatar da hadin kan kasa, hakkin dan kasa da mutunta doka.
“Yayin da muke tunawa da wannan rana mai tarihi, muna karfafa wa kowane dan Najeriya gwiwa ya ci gaba da bin doka, kare matakan da ke rike da dimokuradiyyar mu, ya cewa karfin kowace dimokuradiyya yana hannun halayen ‘yan kasa,” in ji shi.
Ya kara karfafa ‘yan Najeriya da su yi tunani kan tsarin dimokuradiyyar kasar da kuma ba da gudummawa mai kyau wajen korfafa ta da kara hadin kan kasa.
Ana gudanar da ranar dimokuradiyya a kowace shekara a ranar 12 ga Yuni don karrama marigayi Cif Moshood Kashimawo Olawale Abiola da zaben shugaban kasa na 12 ga Yuni, 1993, wanda ake ganin shi ne zabe mafi gaskiya da adalci a tarihin Najeriya.













































