Hukumomin kula da harkokin wutar lantarki da hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya NERC sun amince da nadin da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) ya yi na sabon Manajan Darakta.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa amincewar ya biyo bayan sake fasalin DisCos da Gwamnatin Tarayya ta yi, sakamakon kwace DisCos guda 3 da Bankin Fidelity ya yi wanda na kamfanin KEDCO na cikin su.
Hakan ya kai ga rusa kwamitin gudanarwa na kamfanin KEDCO.
A wata sanarwa da Babban Jami’in yada labarai na Kamfanin, Ibrahim Sani Shawai, ya fitar a ranar Alhamis, ta tabbatar da lamarin.

A cewar sanarwar, daga yanzu Dangana ne zai ci gaba da Jan ragamar kamfanin.
Haka kuma, shugabannin sun amince da Ambasada Hassan Tukur a matsayin shugaban hukumar gudanarwar.
Sauran mambobin kwamitin su ne; Mista Nelson Ahaneku da Injiniya Rabiu Suleiman da Mista Amaechi C. Aloke da Dakta Bashir Gwandu.
Jim kadan bayan Kama aiki, sabon Manajan Daraktn ya baiwa abokan hulda da masu ruwa da tsaki tabbacin gudanar da ingantattun ayyuka da samar da wutar lantarki a Kano, musamman bayan kammala ayyukan da ake ci gaba da yi na fadada hanyoyin rarraba wurar.












































