‘Yar wasan tawagar Najeriya da kungiyar Barcelona, Asisat Oshoala, ta lashe kyautar zama gwarzuwar ‘yar wasan nahiyar Afirka ta kwallon kafa ta Mata.
‘Yar wasan ta Super Falcons, ta zama ‘yar wasa Tilo da ta lashe gasar har sau Biyar.
A baya ‘yar wasan ta zama gwarzuwar Afirka a shekarun, 2014, 2016, 2017, 2019, da Kuma wannan shekarar ta 2022.
Bayan karramata a matsayin gwarzuwar Yar wasan ta bana Asisat, tace:
“Dare ne mai tarihi a gare ni kuma ina so in gode wa duk wanda ya taimaka mini a cikin sana’ata. Kakar wasanni ta 2021/2022 ta kasance mai matukar muhimmanci a gare ni.
“Na gode wa takwarorina na Barcelona FC da kuma kungiya ta Super Falcons, da suka nuna wa Afirka yadda za ku iya juriya a wasan kusa da na karshe da Morocco a ranar Litinin. “Na sadaukar da wannan kyautar ga Super Falcons,” in ji Oshoala.

A halin da ake ciki kuma Sadio Mane na Senegal shi ma ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na Nahiyar Africa waro CAF, inda ya lashe kyautar a karo na biyu.
Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa Oshoala ta fice daga gasar cin kofin Afrika ta mata WAFCON da ake yi a kasar Morocco sakamakon samun rauni da ta yi.
Ta samu rauni ne a wasan farko da Najeriya ta buga da Afirka ta Kudu. Bayan da kungiyar ta sha kashi a hannun Morocco a bugun daga Kai sai mai tsaron raga a wasan kusa da na karshe na gasar, yanzu haka dai Super Falcons za ta buga wasa da kasar Zambia a wasa na uku a ranar Juma’a.













































