Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma (NWGF) ta shirya tattaunawa kan manufofi a Kano kan yadda za a rage talauci ta fuskoki da dama ta hanyar karfafa tsarin dogaro da kai da samar da sabbin hanyoyin tattalin arziki.
Taron wanda ya kun shi masu tsara manufofi, abokan hulda na cigaba da kwararru daga jihohi 7 na Arewa maso Yamma, inda suka tattauna kan dabarun da za su taimaka wajen yaki da talauci ta fuskoki da dama ta hanya mai daurewa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa taron ya ba da muhimmanci musamman ga yara, mata, da sauran kungiyoyin da ke cikin mawuyacin hali a Arewa maso Yamma.
Da yake kaddamar da tattaunawar a Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ya kamata a kalli mata kan Figaro da kai ba kawai a matsayin taimako ba, har ma a matsayin zuba jari da dabarar da za ta inganta jama’a, kwanciyar hankali, da cigaban tattalin arziki.
Mataimakin Gwamnan, Murtala Sule Garo ne ya wakilce shi, inda ya bayyana matakan da Kano ta dauka don samar da damarmakin dogaro da kai ciki har da “Social Protection Directorate 2025) da ke karkashin Ma’aikatar Jin Kai da Rage Talauci.
Ya ce: “Jihar na ci gaba da zuba jari a ilimi, lafiya, koyon sana’a, karfafa matasa, da sauran shirye-shiryen taimako da ke nufin inganta rayuwar jama’a.
Da take jawabin maraba, Darakta Janar ta (NWGF), Maryam Yahaya ta ce tattaunawar wani muhimmin lokaci ne ga yankin.
Ta kara da cewa duk da yawan jama’a, gina dan adam da samuwar tattalin arziki, yankin Arewa maso Yamma na ci gaba da fuskantar talauci ta fuskoki da dama, rashin samun damar lafiya, rashin tsaro, da karuwar yara da ke barin makaranta.
A cewarta, kalubalen da suka dabaibaye iyakokin jihohin yanking, wadanda kuma suna bukatar daukar mataki da hadin gwiwar. Inda ta bukaci a kalli samar da hanyoyin dogaro da kai a matsayin na zuba jari a kwanciyar hankali, don samar da makomar yankin.
A sakonsa ga mahalarta taron, mataimakin wakilin UNICEF, Dr Rownak Khan ya bayyana manyan kalubalen da yara ke fuskanta a Arewa maso Yamma, ciki har da yawan mutuwar mata masu juna biyu, rashin abinci mai gina jiki da karancin samun damarmaki masu muhimmanci.
Wani mahalarta, Muhammad Haruna, ya shaida wa NAN cewa yana da kyakkyawan fata kan yuwar karfafa hadin gwiwar yanki.
Wata mahalarta, Halima Yusuf, ta jaddada muhimmancin manufofi masu dauke aiki da kowa da shirye-shiryen al’umma wajen tabbatar da shirye-shiryen da manufofin shirin. NAN












































