Kungiyar Sinawa ‘yan kasuwa a Najeriya tayi Allah wadai da laifin da dan China ya aikata na yi wa Ummita yanka rago

InCollage 20220917 094426757 1024x1024 1 750x430 1
InCollage 20220917 094426757 1024x1024 1 750x430 1
Kungiyar Sinawa ‘yan kasuwa a Najeriya wato CBCAN, karkashin jagorancin Wakilin Mutanen China a Kano, Mr. Mike Zhang ta jajantawa iyalan Ummita, tare da yin Allah wadai da babban laifin da Geng Quanrong dan China ya aikata na yi wa Ummita yanka rago.

Jaridar solacebase ta rawaitu cewa dan chana ya kashe Ummulkulthum Buhari da wuka, ranar Juma’a a gidansu dake Janbulo Dorayi Babba a karamar hukumar Gwale cikin jihar Kano.

A cikin wata sanarwa dake dauke da sa hannun Mr. Guang Lei Zhang, da aka fitar da ita a ranar Litinin, ‘yan chanan suniy Allah wadai da wannan ta’addancin kuma a bawa doka dama tayi aikin ta.

“Allah ya jikan Ummita, ya gafarce ta ya kuma sa ta huta, Allah ya kara zumunci a tsakanin Sinawa da Hausawa.” Inji sanwarwar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here